Search
Subscribe
Gwamna Lalong ya rantsar da sababbin kwamishinoni

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato

Gwamna Lalong ya rantsar da sababbin kwamishinoni

Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Bako Lalong ya rantsar da sababbin kwamishinonin jihar 23 a gidan Gwamnati da ke Jos.

Da yake jawabi a wajen bikin Gwamna Lalong ya gargadi kwamishinonin kan su yi aiki da tsarin gwamnatinsa na ceto jihar, ko kuma ya sauke su.

Ya ce kwamishinonin su dauki wannan dama da aka ba su a matsayin wani babban nauyi, da aka dora mUsu. Don haka su yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun nuna kishin kasa, ta hanyar rike gaskiya yayin gudanar da ayyukansu.

Gwamna Lalong ya yi kira ga kwamishinonin su hada kai da manyan sakatarori da daraktoci da sauran ma’aikatan ma’aikatun da aka tura su, domin ganin an samu nasarar tafiyar da tsare-tsaren ayyukan wannan gwamnati.

Sababbin kwamishinonin da aka rantsar tare da raba musu ma’aikatu, sun hada da Mista Dan Manjang, Watsa Labarai da Pam Bot Mang Ma’aikatar Ayyuka da Bictor Lapang, Matasa da Wasanni da Elizabeth Wapmuk Ma’aikatar Ilimin Makarantun Sakandare da Yakubu Dati, Kasa da Safiyo da Sylbanus Tapgun, Kananan Hukumomi da Masarautu da Barista Rimben Bitrus Zulfa, Ma’aikatar Gidaje.

Sauran su ne Ibrahim Sa’ad Bello, Albarkarun Ruwa da Barista Chrisantus Ahmadu, Shari’a da Dokta Nimkong Lar Ndam, Lafiya da Alhaji Dayyabu Garga Ma’aikatar Bunkasa Birane da Dokta Istifanus Finangwai, Ma’aikatar Gona da Tamakat Weli, Yawon Bude Ido da Dokta Regina Soemlat Ma’aikatar Kudi da Kakmena Goteng Audu Ma’aikatar Ilimi   Mai Zurfi da Idi Yakubu Bamaiyi Ma’aikatar Muhalli da Dakur Jude Idi Ma’aikatar Ma’adanai da Cif Sylbester Wallangko Ma’aikatar Kasafi da Tsara Tattalin Arziki da Dung Musa Gyang, Kimiya da Kere-Kere da Da Jerry Irmiya Werr, Ayyuka na Musamman da Muhammad Muhammad Abubakar Ma’aikatar Sufuri da Rebecca A. Sambo Ma’aikatar Al’amuran Mata da kuma Joseph Abe Aku Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin