✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Lalong ya tabbatar da yin adalci ga kowa

Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya yi alkawarin ci gaba da tabbatar da rashin nuna banbanci da san zuciya ga duk ’yan jihar ta…

Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya yi alkawarin ci gaba da tabbatar da rashin nuna banbanci da san zuciya ga duk ’yan jihar ta fannin qabila ko addini ko kuma banbancin siyasa. Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan rantsar da shi da aka yi jiya Laraba a matsayin Gwamnan jihar karo na biyu.

Gwamna Lalong, ya ce jihar Filato ta kasance jiha ce da take da kabilu da dama, sannan ya ce a wannan karon za a rarraba ayyukan jihar ga inda aka fi bukata. Hakan zai tabbatar da yin adalci ga jama’ar da suka kada kuri’ar su don samun ci gaba a jihar.