✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Lalong ya zabi sakataren ‘yan agajin Izala Kwamishina

Sakataren ‘Yan agajin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah ta Kasa Malam Muhammad Muhammad Abubakaryana daya daga cikin sunayen sababbin Kwamishinoni guda 23 da gwamnan…

Sakataren ‘Yan agajin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah ta Kasa Malam Muhammad Muhammad Abubakaryana daya daga cikin sunayen sababbin Kwamishinoni guda 23 da gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, ya gabatarwa majalisar dokoki ta Jihar Filato domin tantancewa.

Sunayen sababbin Kwamishinonin ya nuna cewa, akwai sunayen tsofaffin Kwamishinoni 11 da aka sake dawo da su. A yayin da aka kawo sababbin sunayen Kwamishinonin 12.

Da yake karantawa ‘yan majalisar dokokin sunayen sababbin Kwamishinonin a jiya Talatar, shugaban majalisar Honarabul Ayuba Abok ya bayyana cewa, sunayen tsofaffin Kwamishinonin 11 da aka sake dawo da su, sun hada da  Alhaji Dayyabu Garga da Yakubu Dati da Mista Dan Manjang da Idi Usman Bamayi da Victor Lapang da Regina Soemlat da Tamwakat Weli da Sylvester Wallangko da Elizabeth Wapmuk da  Dakur Jude Eli da kuma Pam Botmang.

Sunayen sababbin Kwamishinonin 12 da aka gabatar sun hada da Chrisantus Ahmadu da  Muhammad Muhammad Abubakar da Jerry Werr da Sambo Rebecca Adar da Abe Aku da Dung Musa Gyang da Tapgun Sylvanus da Nimkong Lar-Ndam da Kak ‘Mena Goteng Audu da Ibrahim Saad Bello da Rimven Bitrus  Zulfa da kuma Hosea Istifanus Finangwai.

Majalisar ta sanya ranar 23 ga wannan wata a matsayin ranar da zata fara tantance sunayen wadannan Kwamishinoni.