✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna mai jiran gado ya gana da Gwamna mai barin gado a Jihar Oyo

Gwamna mai jiran gado a Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde ya shafe makon jiya yana ziyartar wadansu manyan mutane a ciki da wajen jihar. Zababben…

Gwamna mai jiran gado a Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde ya shafe makon jiya yana ziyartar wadansu manyan mutane a ciki da wajen jihar. Zababben Gwamnan ya fara ziyarar Fadar Mai martaba Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji ne inda ya shaida wa Sarkin cewa “A lokacin da na zo yakin neman zabe a fadarka ka yi mani addu’a cewa ni ne zan zama sabon Gwamna da yardar Allah, to ga shi Allah Ya karbi addu’arka na yi nasarar zama Gwamna da goyon bayan dukan al’ummar Jihar Oyo.”

Ziyarar da ba a zata ba ita ce wacce Gwamnan mai jiran gado Seyi Makinde ya kai wa Gwamna mai barin gado Abiola Ajimobi a ofishinsa da ke Agodi a Ibadan, inda suka rika yin raha da murmushi tare da tattaunawa kan yadda za a tafiyar da mulkin jihar da Jam’iyyar PDP tayi nasarar karba daga APC a zaben da ya gabata.

Injiniya Seyi Makinde wanda yake tare da Mataimakinsa Alhaji Rauf Olaniyan da sauran jigogin Jam’iyyar  PDP sun kai irin wannan ziyara ga tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a garin Abeokuta hedkwatar Jihar Ogun inda tsohon Shugaban ya ba shi shawarwari kan salon mulki da ya kamata ya yi a Jihar Oyo, ba kamar yadda gwamnati mai barin gado ta yi fatali da wasu harkokin mulki a jihar na tsawon shekara 8 a karaga ba. “Kada ka kasance mai girman kai, kuma kada ka kuskura ka yi mulkin dimokuradiyya don azurta aljihu, ka gudanar da mulkinka kamar yadda dimokuradiya ta shimfida musamman wajen nemo ’yan kasuwa da za su zuba jari don bunkasa ci gaba a Jihar Oyo,” inji Obasanjo.

A ranar Juma’ar da ta gabata Seyi Makinde ya ziyarci babban masallacin Ibadan da ke Oja Oba inda aka yi Sallar Juma’a tare da shi a matsayinsa na mabiyin addinin Kirista. Jim kadan bayan kammala Sallar wadda Babban Limamin Ibadan Sheikh Abdulganiyu Agbotomokekere ya jagoranta, zababben Gwamnan ya shaida wa dubban Musulmin da suka halarci masallacin cewa, “Na zo ne domin nuna godiyata da goyon bayan da kuka ba ni. Ina tabbatar muku cewa ba za ku yi nadamar yin amfani da kuri’unku wajen zabena ba kuma gwamnatina ba za ta fifita wani addini a kan wani ba domin yin haka ne kadai zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummar Jihar.”

A lokacin da yake jawabi ga wakilan Majalisar Olubadan su 21 da gwamnati mai barin gado ta daukaka darajarsu daga hakimai zuwa sarakuna, zababben Gwamnan, wanda dan asalin Ibadan ne ya ce, gwamnatinsa ba ta da nufin rage matsayinsu zuwa hakimai kamar yadda ake baza jita-jita amma ya ce, zai yi duk abin da yake iyawa wajen ganin ya hada kan wakilan Majalisar Masarautar Ibadan.

Wannan jawabi ya faranta wa sarakunan a karkashin jagorancin Otun Olubadan Sanata Lekan Balogun da suka kai wa sabon Gwamnan gaisuwar taya shi murna a gidansa da ke Ikolaba  a birnin Ibadan.