Da Dumi Dumi

Gwamna Masari ya ba ’yan bindiga kwana biyu su mika wuya

Gwamna Jihar Katsina Aminu Bello Masari

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ba ’yan bindiga kwana biyu da su mika wuya tare da sako duk mutanen da ke hannunsu ko su fuskanci fushin gwamnati.

Gwamna Masari ya bayyana haka ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar Dokta Mustafa Inuwa wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Tsaro da Sasanci na Jihar bayan taron da suka yi da Babban Kwamadan Rundunar Soji ta 8 da ke Sakkwato Janar Aminu Bande da wakilan wadanda aka yi sasanci da su da kuma wadanda har yanzu ba su rungumi sasancin ba.

Dokta Mustafa Inuwa ya ce wannan shi ne zama na karshe da ’yan bindiga, saboda haka, “Su wadanda suka karya yarjejeniyar da aka yi da su, su sani cewa gwamnati ta ba su kwana biyu su yi mika wuya kuma su sako duk mutanen da suke hannunsu ko kuma su fusksnci fushin gwamnati ta hanyar nuna musu irin nata karfin,” inji shi.

A jawabin Janar Aminu ya ce a shirye sojoji suke don tunkarar  ’yan ta’addan muddin suka ki mika wuya.

Matsalar tsaro a yanzu na neman zama  ruwan-dare a  Katsina kuma maharan kullum kara dabarun kai hare-haren suke yi ta hanyar amfani da wadansu batagari a cikin al’umma.

ADVERTISEMENT

An yi wannan taron ne a ranar Talatar da ta gabata.

Share