✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Masari ya gabatar da kasafin kudin 2020 Naira biliyan 249  

A yau Laraba ne, Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya gabatarwa Majalisar Dokokin jahar da kasafin kudin shekarar 2020 na Naira bilyan dari…

A yau Laraba ne, Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya gabatarwa Majalisar Dokokin jahar da kasafin kudin shekarar 2020 na Naira bilyan dari 2 da 49 da milyan dari 463 da dubu dari 829 da Naira dari 250 (N249,463,829, 250.00). Taken kasafin kudin na 2020 shi ne, ‘Waiwayen baya da Ayyukan ci gaba’.

Kazalika ya baiyana cewa, kasafin kudin na 2020. Nada Naira biliyan 75 dd milyan 579 da dubu 865 da dubu 990 daidai ga ayyukan yau da kullum yayin da manyan ayyuka ke da kason Naira bilyan 173 da milyan 883 da dubu 963 da dari 260. Sashen ilmi ne ke da kaso mafi tsoka na sama da Naira bilyan 24, sai sashen lafiya da hanyoyi nada sama da biliyan 23, yayin da noma da kiwo ke sama da bilyan 13.

Har’ila yau, Gwamna Masari ya ce, babu wasu sabbin ayyukan da zasu yi a yanzu har sai sun kammala wadanda suka faro basu karasa ba. Sannan kashin yawan kudin da za’a kashe a wajen manyan ayyuka sun yi daidai da kashi 69.70 a cikin 100 na yawan jimlar kasafin kudin.