✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Masari ya rantsar da sababbin kwamishinoni  

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya rantsar da kwamishinoni 17 da za su jagorancin ma’aikatun jihar.…

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya rantsar da kwamishinoni 17 da za su jagorancin ma’aikatun jihar.

A jawabinsa bayan rantsar da kwamishinonin da masu bada shawara da manyan sakatarori, Gwamna Aminu Masari ya ce, an yi nade-naden ne domin ganin cewa an hada kai tare da bayar da gudunmawar da za ta ciyar da jihar gaba.

Don haka ya bukaci wadanda aka nada su yi aiki yadda ya kamata don ci gaban Jihar Katsina. “Sannan ku sani cewa, za a rika sa ido a kan yadda kuke tafiyar da harkokin mulki domin tabbatar da cewa, ana gudanar da aikin gwamnati yadda doka ta tsara. Ba yin sakaci ko watsi da aikin ofis. Yana da kyau ku sani cewa batun harkokin kudi, ba a jihar nan kadai ba, har a kasa baki daya abu ne da ke bukatar kula tare da yin amfani da abin da ke hannu,” inji shi.

Sababbin kwamishinonin 8 da aka nada sun hada da tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar a lokacin PDP wanda ya yi canjin sheka zuwa APC Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo wanda aka ba Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu, sai tsohon Kwamishina a lokacin PDP Alhaji Musa Adamu Funtuwa wanda aka kai Ma’aikatar Albarkatun Ruwa. Sauran su ne tsohon dan Majalisar Wakilai, Alhaji Sani Danlami da zai jagoranci Ma’aikatar Matasa da Wasanni. Sai tsohon Manajan Hukumar Raya Birane da Karkara Alhaji Usman Nadada, Ma’aikatar Kasa da Safiyo. Kassim Mutallab Funtuwa shi zai jagoranci Ma’aikatar Kudi yayin da Abdulkarim Yahaya Sirika zai jagoranci Ma’aikatar Watsa Labarai. Injiniya Yakubu Nuhu Danja, Ma’aikatar Lafiya,  Rabi’a Muhammad za ta jagoranci Ma’aikatar Harkokin Mata.

Daga cikin tsofaffin da aika maido akwai Tasi’u Dandagoro wanda ya sake komawa Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri, sai Mukhtar Kado, Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu da Yawon Shakatawa. Farfesa Badamasi Lawal Chiranci ya sake komawa Ma’aikatar Ilimi. Mustafa Mahmud, Ma’aikatar Raya Karkara da Harkokin walwala. Hamza Mohammad Faskari, Ma’aikatar Muhalli, yayin da Abdulkadir Zakka ya zama Kwamishinan Ayyuka na Musamman.