✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Mutawalle ya yi wa Fulani fursunoni 100 afuwa

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Mutawalle, ya ce gwamnatin jihar zata yi wa Fulani fursunoni 100 afuwa a matsayin wata hanya na tattaunawa da ‘yan…

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Mutawalle, ya ce gwamnatin jihar zata yi wa Fulani fursunoni 100 afuwa a matsayin wata hanya na tattaunawa da ‘yan bindigar jihar don samun zaman lafiya.
 
Fursunonin wadanda Fulani ne da aka tsare a gidan yarin Gusau wanda ake tuhumar su da laifukan da suka hada da: fashi da makami, yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kuma satar shanu. Ana saran duk za a sake su kafin karshen wannan makon.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilin shugabannin unguwannin Fulani, wanda su ke shiga tsakanin tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnatin jihar da ‘yan bindigar.

Gwamna Mutawalle, ya yi Allah wadai da yadda ake bata sunan Fulani ba wai a jihar ba kadai har da sauran yankunan kasar, inda ake kallon su a matsayin ‘yan ta’adda.