✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna ne uban ’yan PDP a Gombe ba Goje ba – Jalo

Mataimakin Kakakin Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Abdullahi Ibrahim Jalo ya ce Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ne uban ’yan PDP a Jihar Gombe…

Barista Abdullahi Ibrahim JaloMataimakin Kakakin Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Abdullahi Ibrahim Jalo ya ce Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ne uban ’yan PDP a Jihar Gombe ba Sanata danjuma Goje kamar yadda ya fada ba.

Barista Ibrahim Jalo ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a Gombe don mayar da martani kan kalaman tsohon Gwamnan Sanata danjuma Goje, inda ya ce Sanatan “Ya tara matasa dauke da takubba da adduna suna yi wa mutane barazana a gari bayan shi ba Gwamna ba ne inda yake so ya sake lalata matasan bayan an farfado da tarbiyyarsu. Kamar kuma yadda ya ce a lokacinsa ne ya kwace mulki daga hannun ANPP ai ba kwace mulki ya yi ba, Allah ne Ya karbi mulki daga hannun Hashidu a ANPP Ya ba shi kuma ai ba shi kadai ya yi wannan gwagwarmayar ba ni ma ina cikin wannan tafiyar domin na sa iya siyasata da kudina.”
Barista Jalo ya ce ba wanda yake fada da Sanata Goje shi ne ya fito yake neman fada domin yana cewa shi ne uban duk ’yan PDP na Gombe, “abin da nake so a sani ba kwace mulki muke yi ba zabe aka yi muka ci zabe amma dai na yarda da shi ya jagorance mu a lokacin.”
Ya ce laifin Goje shi ne ya fito ya ce akwai sabuwar PDP har ma ta kwace Gombe, ya ce shi fa Sanata ne mai ci kuma mutum ne mai ilimi ya kamata ya san akwai doka, wacce ita ta kai shi ya wakilci mutane kuma a PDP ya ci zabe wacce Bamanga Tukur yake shugabanta ba sabuwar PDP ba, ashe kuwa in haka ne daga furta wannan magana tasa ya saba doka.
Barista Jalo, za su rubuta takardar kuka ga uwar jam’iyyarsu a PDP domin a kira Sanata Goje ya amsa tambayoyi kana bin da ya yi na alkanta kansa da sabuwar PDP. “Kuma yana da kyau mutane su sani tsarin mulkin PDP ya tabbatar da cewa uban jam’iyya a Jihar Gombe shi ne Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo, Goje ya zo ne watakila da wata manufa ta komawa Jam’iyyar APC, hakan takalar fada ne don ba a taba jin gwamnonin da suka yi shekara takwas suka sauka suka kawo wadanda suka gaje su suna irin wannan fada da su ba,” inji shi.