✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Tambuwal ya kaddamar da raba Naira biliyan 4 ga masu sana’o’in hannu

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da rabon tallafin Naira dubu 20 ga mutum dubu, maza 500 da mata 500 a karkashin…

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da rabon tallafin Naira dubu 20 ga mutum dubu, maza 500 da mata 500 a karkashin shirin bayar da tallafin kanana da matsakaitan sana’o’i da aka sanya wa suna Micro Businesses Incentibe Fund (MBIF).

Gwamnatin Tambuwal ta kirkiro shirin ne don rage radadin talauci da samar da sana’a ga mutanen jihar, kuma an kaddamar da shirin ne a garin Balle da ke Karamar hukumar Gudu, bayan nan ya tafi kananan hukumomin Tureta da Sabon Birni.

Gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan hudu ga shirin inda mutum dubu 200 ne za su amfana da shi a kananan hukumomi 23 da ke jihar.

Kowace karamar hukuma mutum 1,000 ne za su amfana.

Sai dai kaddamar da shirin ya bar baya da kura ganin yadda aka ga Gwamna Tambuwal ya je garin Balle don soma aikin ba tare sanin ranar da Majalisar Zartarwar Jihar ta zauna domin tattauna wannan kudiri don ba da dama ga Gwamna ya cire kudin da yadda za a zakulo wadanda za su ci moriyar kudin, da kuma mafitar kudin don sanar da mutanen jiha da kasa baki daya.

Kan wannan tirka-tirka wakilinmu ya nemi jin ta bakin Mai ba Gwamnan Shawara kan Watsa Labarai, Malam Muhammad Bello, inda ya ce, “Naira biliyan hudu ba kudi ne a kasa a ajiye ba a hankali za a rika tsakura ana yi.”

Da aka tambaye kan Gwamna na da damar taba kudin ko Majalisar Zartarwa ba ta zauna ba,  sai ya ce, “Ina kyautata zaton haka, amma ba zan iya cewa haka ne ba, bin doka abu ne mai muhimmanci wurin gudanar da gwamnati, Gwamna a matsayinsa na mai bin doka da oda na san ba zai yi wa doka karan-tsaye ba. Zai yi abin da ya dace.”