Da Dumi Dumi

Gwamna Yahaya Bello zai kai ga nasara – Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Adams Oshiomhole da wadansu gwamnonin APC sun halarci kaddamar da yakin neman zaben Gwamnan Jihar Kogi a ranar Lahadin da ta gabata, inda Farfesa Osinbajo ya ce yana da yakinin Gwamna Yahaya Bello sai samu nasara a zaben na ranar 16 ga watan nan. Farfesa Osinbajo wanda ya mika wa Gwamna Yahaya Bello da Mataimakinsa Edward Onoja tutar Jam’iyyar APC ya ce yana da yakinin Jam’iyyar APC za ta kai labari a zaben jihar.  Shugaban APC na Kasa Adams Oshiomhole ya fada wa taron cewa “Idan kun san halin da jihar nan take ciki lokacin mulkin PDP, da yadda take a yau, za ku fahimci cewa akwai bukatar a sake zaben Yahaya Bello don ya ci gaba da mulki.”

Mista Oshiomhole ya kara da cewa “Bello ya yi aiki don haka nake kira gare ku da ku zabe shi don ba zai ba ku kunya ba.”

A jawabin Gwamna Yahaya Bello ya fada wa taron cewa su dage wajen ganin sun kai ga nasara. Gwamna Bello ya bayyana cewa APC za ta yi yakin neman zabe gida-gida a fadin jihar domin ta zarce a mulki. Daga cikin wadanda suka halarci kaddamar da yakin neman zaben akwai Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule da na Kwara Abdulrahman Abdulrazak da Mai Mala Buni na Yobe da Sani Bello na Neja, da Minista a Ramatu Tijjani da ’yan majalisa da sauran manyan ’ya’yan Jam’iyyar APC daga ciki da wajen jihar.

Share