✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Zulum ya gana da ’yan Keken Napep

Bayan jita-jitar da ta gama gari na cewa Gwamnatin Jihar Borno za ta hana aikin Keke Napeep a jihar Borno, a ranar Talatar da ta…

Bayan jita-jitar da ta gama gari na cewa Gwamnatin Jihar Borno za ta hana aikin Keke Napeep a jihar Borno, a ranar Talatar da ta gabata, Gwamnan Jihar ya yi wata ganawa da shugabannin masu sana’ar a Maiduguri.

Taron ya gudana ne a sakatariyar Musa Usman, inda Gwamna Zulum ya bawa masu sana’ar tabbacin yin gyara a cikin sana’ar, sannan ya ce daga “cikinku masu wannan sana’ar ai akwai masu digiri, wanda ya kamata a samar musu da ayyukan yi, tare da tallafa musu,” sannan ya kara da cewa gwamnatinsa ba ta da niyyar hana kowa sana’arsa amma ya zama dole a tsabtace harkar.

Wasu masu sana’ar da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana gamsuwarsu kan yin gyarar domin inganta harkar.

Abdullahi Musa ya ce ya shafe sama da shekara 7 yana sana’ar, kuma su a shirye suke su bi duk wata doka da aka tsara musu, “domin a gaskiya akwai batagari a cikin sana’ar.” Sannan ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa musu.

Shi kuwa Alhassan Muhammad cewa ya yi gaskiya kamata ya yi gwamnati ta sake tunani na hana su bin wasu manyan hanyoyi a fadin jihar, inda ya ce a maimakon yin haka kamata ya yi a rika shirya musu taron fadakarwa a kan sanin ka’idojin bin manyan hanya, domin gaskiya kashi 80 na masu yin wannan sana’a ba su da wani ilimin bin manyan hanya.

Da Aminiya ta tuntubi Shugaban masu sana’ar na Adalci, Maikano Muhammad Bandur ya ce hakika akwai matsala a cikin masu sana’ar, amma wannan tsari na inganta sana’ar zai karawa sana’ar daraja.