✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Zulum ya kwana a sansanin gudun hijira

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ga sansanin ’yan gudun hijira, inda ya kwana tare da su, ya kuma raba musu…

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ga sansanin ’yan gudun hijira, inda ya kwana tare da su, ya kuma raba musu barguna domin maganin sanyi, inda iyalai 1,675 suka amfana.

Gwamna ya kai ziyarar ba-zata ce a sansanin ’yan gudun hijira da ke matsugunin masu yi wa kasa hidima da ke Maiduguri, inda ya tattauna da ’yan gudun hijirar domin sanin halin da suke ciki.

Gwamnan ya raba musu tabarmi da barguna da rigunan sanyi sannan ya ba su tabbacin za su koma garuruwansu. Gwamnan  ya ce zai yi duk abin da ya kamata don ganin kowa ya koma gida, tare da ba su tallafi domin su zama masu dogaro da kansu.

Sai ya sake ba su tabbacin kudirin Gwamnatin Tarayya n kawo karshen Boko Haram, inda ya kuma yaba wa sojoji don irin kokarin da suke a yakin da ake da Boko Haram, sannan ya gargade su kan su kai rahoton duk wani mutum da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro.

Kuma ya ce Gwamnatin Borno za ta gina rukunin gidaje 10,000 a yankunan karkara da birane domin tabbatar da ganin ’yan gudun hijirar sun koma gidajensu, tare da rufe sansanonin gudun hijira da ke Maiduguri da Jere a bana.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da rundunar maida martanin gaggawa da ta kunshi sojoji da ’yan sanda da maharba da sauran jami’an tsaro domin ci gaba da yakar Boko Haram.

Daga nan sai Gwamnan ya bada motocin sintiri 70, sannan ya umarci maharba da ’yan bangasu rika yin sintiri a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa don kara tabbatar da tsaro.

An kaddamar da shirin ne a ranar Juma’ar da ta gabata a kofar Fadar Shehun Borno.

Gwamna Zulum ya ce, “Ina sanar da al’ummar kasar nan cewa Shugaban Kasa ya bada umarnin a gina rukunin gidaje 10,000 a cikin shirin Gwamnatin Tarayya na sake gina Jihar Borno.”

A jawabin Kwamandan Rundunar Tsaro ta Lafiya Dole, wanda Mataimakinsa Manjo Janar MG Ali ya wakilta, ya gode wa Gwamnatin Jihar Borno kan irin taimakon da take ba jami’an tsaron wajen ganin an kawo karshen Boko Haram.