✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Bauchi ya kamu da Coronavirus

Sakamakon wani gwaji da aka yi ya nuna cewa Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammmed, yana dauke da cutar Coronavirus. A wata sanarwa da babban mai…

Sakamakon wani gwaji da aka yi ya nuna cewa Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammmed, yana dauke da cutar Coronavirus.

A wata sanarwa da babban mai bai wa gwamnan shawara a kan kafofin yada labarai Mukhtar Gidado ta tabbatar da hakan. Inda ya ce bayan gwajin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta yi an tabbatar da mutum shida ne suka kamu da cutar.

A ranar Litinin ne aka shiga zaman zullumi a Bauchi bayan da gwamnan jihar, Bala Mohammed, da kwamishinoninsa guda biyu suka killace kansu sakamakon mu’amala da dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda aka tabbatar yana dauke da cutar Coronavirus.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta sanar da cewa, zuwa yanzu mutum 44 ne suka kamu cutar Coronavirus a Najeriya, mutum 2 sun warke yayin da daya ya rasu, saura mutum 41 da suke da cutar.