Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Gwamnan Borno ya kwana biyu a Monguno don aza harsashin gina gidajen ’yan gudun hijira

Gwamnan Borno ya kwana biyu a Monguno don aza harsashin gina gidajen ’yan gudun hijira

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara Monguno inda ya shafe kwana biyu a garin.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Malam Isa Umar Gusau ya aike wa kafafen watsa labarai.

Sanarwar ta ce a yayin ziyarar, Gwamna Babagana Zulum ya aza harsashin ginin gidaje 1,000 domin ’yan gudun hijira da suke  zaune a wasu makarantun jihar.

Gwamnan ya kuma aza harsashin ginin wata Kwalejin Musulunci da za ta samar wa mutum dubu 10, da ke da ilimin addinin Musulunci damar samun diploma a ilimin zamani.

Akwai ’yan gudun hijra dubu 89 da ke zaune a Monguno wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Kwamishinan Sake Gina Jihar Borno Injiniya Mustapha Gubio ya ce an aza harsashin gina rukunin gidajen ne domin samar wa ’yan gudun hijrar wurin zama, inda ya ce hakan zai ba makarantun da ’yan gudun hijrar suka mamaye damar komawa bakin aiki.