✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Delta ya kamu da coronavirus

Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa ya kamu da cutar coronavirus. Okowa ya sanar da kamuwarsa da matarsa da curtar a sakon da ya wallafa a…

Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa ya kamu da cutar coronavirus.

Okowa ya sanar da kamuwarsa da matarsa da curtar a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

“Ni da mai dakina mun kamu da COVID-19 amma har yanzu da kwarinmu a inda muka killace kanmu”, inji shi.

Kamuwar gwamnan na zuwa ne kwana biyar bayan ya sanar da harbuwar diyarsa wadda ta sa sauran iyalansa suka fara killace kansu.

Okowa ya shiga sahun takwarorinsa gwamnoni da suka kamu da cutar ne washegarin ranar da Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya kamu da cutar.

Zuwa yanzu shi ne na shida a cikin gwamnonin Najeriya da suka kamu da cutar.