✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Edo ya nemi ’yan sanda su kama Oshiomhole

Rikicin siyasa da ke gudanwa a Jam’iyyar APC a Jihar Edo ya dauki sabon salo a farkon makon nan, inda Gwamnan Jihar Godwin Obaseki ya…

Rikicin siyasa da ke gudanwa a Jam’iyyar APC a Jihar Edo ya dauki sabon salo a farkon makon nan, inda Gwamnan Jihar Godwin Obaseki ya bukaci Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Muhammed Adamu da kuma Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta Kasa (DSS), Alhaji Yusuf Bichi, su hanzarta kama Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Kwamred Adams Aliyu Oshiomhole bisa abin da ya kira “yin kunnen shegu da umarnin ’yan sanda na haramta gangamin siyasa da kuma tayar da zaune tsaye a jihar.”

Da yake ganawa da manema labarai a Abuja ta bakin Mataimakinsa, Mista Philip Audu, Gwamna Obaseki ya ce zai gabatar da takardar korafi a kan batun ga hukumomin da abin ya shafa, yana mai cewa Oshiomhole ba ya da damar gudanar da gangamin siyasa a jihar da take karkashin Jam’iyyar APC ba tare da neman sahalewar Gwamnan Jihar ba.

Ya ce: “A takaice, a halin yanzu ina nan a Abuja domin ganawa da Sufeto Janar din. Ina da koke ga Sufeto Janar din ’Yan sanda da Daraktan Hukumar DSS domin ’yan sanda da jami’an DSS su kama Kwamared Adams Oshiomhole, sakamakon yi wa doka karan-tsaye da ya dade yana aikatawa a Jihar Edo.

“Mun haramta gangami siyasa, haka ma Sufeto Janar na ’Yan sanda a cikin wata wasika ya haramta hakan. Oshiomhole ya karya dokar gwamnatin jihar; ya kuma keta umArnin Sufeto Janar yana jin cewa ya fi karfin doka.

“Gare mu a yanzu mun zo nan ne a hukumance domin mika korafinmu ga Sufeto Janar domin mu sanar da shi cewa Oshiomhole fa bai fi karfin doka ba. Lallai ne a kama shi,  saboda yadda ya bijire wa dokar jihar.

“Ya yi gwamna a baya, kuma yana sane da cewa babu wanda ya keta dokokin da ya sanya a matsayinsa na Gwamna, sakamakon ba wai domin sa ba ne, a’a domin al’ummar jihar ne. Yayin da kowa ya bijire wa dokoki, to fa kasar ta zama wata rubabbiyar jamhuriya ke nan, Allah Ya tsare,” inji Gwamna Obaseki.