Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Gwamnan Filato ya zama Shugaban Gwamnonin Arewa

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya samu nasarar zama Shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa su 19.Ya zama shugaban ne sakamakon karshen wa’adin gwamnan jihar Borno Kashim Shettima wanda shi ne yake rike da shugabancin kungiyar Gwamnonin.

Yayin da yake karanta takardar bayan taron da kungiyar ta gudanar Kashim Shatima ya ce, Gwamna Lalong shi zai gaje shi da zarar wa’adinsa ya qare a ranar 29 ga watan Mayun 2019.

ADVERTISEMENT

Sabon shugaban kungiyar Gwamnonin ya mika jawabinsa na godiya ga daukacin gwamnonin da suka daura masa wannan nauyi kuma yasha alwashin ba zai basu kunya ba zai yi aiki tukuru kamar yadda wanda ya gada.

Cikkaken bayanin nan tafe.

ADVERTISEMENT