✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Jihar Oyo ya ba ’yan sanda motoci 100

Gwamnan Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde ya cika alkawarin da ya yi kwanan baya cewa gwamnatinsa za ta tallafa wa rundunar ’yan sandan jihar da…

Gwamnan Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde ya cika alkawarin da ya yi kwanan baya cewa gwamnatinsa za ta tallafa wa rundunar ’yan sandan jihar da sababbin motoci 100 domin kyautata tsaro a jihar. Da yake mika sababbin motocin kirar Kia Rio ga rundunar, Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen kyautata tsaro musamman kula da walwalar jami’an tsaro domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Gwamnan ya ce burin gwamnatinsa ne bullo da sababbin matakan tsaro domin al’ummar jihar da baki masu hada-hadar kasuwanci a jihar su kwanta idanu biyu rufe ba wata fargaba.

“Wannan gwamnati ta dogara ne da ginshiki hudu da tsaro ke cikinsu. Saboda haka muke tabbatar wa aikata miyagun ayyuka su yi nesa ko  su kaurace wa Jihar Oyo, domin jami’an tsaro za su dakile danyen aikinsu,” inji shi.

Gwamnan ya bayar da umarnin sanya na’urorin sadarwa a cikin motocin don taimakawa wajen isar da sakon gaggawa. Ya ce yin haka zai taimaka wa jami’an tsaro gudanar da aikinsu cikin sauki ta yadda za a iya gano miyagun mutane a kankanen lokaci kafin su tsere.

Da yake karbar motocin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu, ya jinjina wa Gwamnan kan alkawarin da ya cika, inda ya ce motocin za su taimaka wa rundunar wajen gudanar da aikin tsaro a jihar.

Kwamishinan ya roki jama’a su ci gaba da taimakawa rundunar da labaran sirri da za su sa a gano maboyar miyagun mutane da kama su tare da gurfanar da su gaban kotu.

Kwamandojin rundunonin tsaro da sarakuna da shugabannin addinai da kungiyoyin masu motocin sufuri da sauran masu ruwa-da-tsaki ne suka halarci bikin da aka gudanar a Sakatariyar Gwamnati da ke Agodi a birnin Ibadan.