✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna El-Rufa’i ya kamu da Coronavirus

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya bi sahun mutanen da ta tabbata sun kamu da cutar Coronavirus. Gwamnan ne ya bayyana hakan da bakinsa…

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya bi sahun mutanen da ta tabbata sun kamu da cutar Coronavirus.

Gwamnan ne ya bayyana hakan da bakinsa a wani hoton bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.

“A farkon wannan makon na bayar da jini don a yi min gwajin Coronavirus”, inji Gwamna El-Rufai, wanda ya kara da cewa, “sakamakon ya fito da maraicen nan, kuma ina bakin cikin shaida maku cewa ya nuna ina dauke da cutar”.

Gwamnan ya kuma ce kamar yadda ka’idojin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) suka tanada tuni ya killace kansa.

Gwamnatin Kaduna na cikin Hukumomin jihohin Najeriya da suka fi takurawa don ganin an dauki matakan hana cutar yaduwa, ciki har da rufe kasuwanni da rufe iyakokin jihar ga baki daya.