Da Dumi Dumi

Gwamnan Kaduna ya nada sabon shugaban hukumar Al’hazai

Mallam Sani Dalhatu Musa

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Ahmed El-rufai, ya amince da nadin Mallam Sani Dalhatu Musa a matsayin sabon shugaba mai kula da hukumar al’hazai ta jihar.

Malam Sani, kafin nadinsa shi ke rike da mukamin jami’an gudanarwa ta hukumar alhazan jihar.

Yana da kwarewa na kusan shekara 20 a aikin hajji inda a lokuta daban daban ya rike mukamin jami’in alhazai na kananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi da sauransu.

Ya kuma rike mukamin kwadinata kafin‎ ya zama jami’in gudanarwa ta hukuma watau (Operations).

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya