✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Legas ya ba da umarnin sake bude makarantu

Daliban makarantun kwana za su koma makaranta ranar 1 ga Nuwamba, 2020

Gwamnatin jihar Legas ta ba da umarnin sake bude makarantu domin ci gaba da karatu a fadin jihar.

Ma’aikatar Ilimin jihar, a sanarwar da ta fitar ranar Alhamis ta fitar, ta ce daliban makarantun kwana za su koma ranar 1 ga watan Nuwamba, ‘yan je-ka-ka-dawo kuma za su koma ranar 2 ga watan Nuwamba.

“Muna fatan ba za a sake samun tsaiko a tsarin karatun bana ba; Gwamnatin jiha ta fi mai da hankali wajen kare rayukan dalibai da malamai.

“Muna kuma sa ran da zarar an dawo karatu babu abin da zai kawo cikas har sai an kammala zangon karatun”, inji sanarwwar.

Kwamishinar ma’aikatar, Folasade Adefisayo, ta shawarci dalibai su mayar da hankali kan karatunsu domin cike gurbin abin da suka rasa tsawon lokacin da suka shafe a gida.

Daga nan sai ta ja hankalin malamai kan su kara jajircewa wajen ba da ilimi nagartacce ga dalibansu.

A makon da ya wuce ne dai Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da sake rufe makarantun jihar saboda yadda zanga-zangar #EndSARS ta rikide zuwa tarzoma a jihar.