Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Gwamnan Legas ya bude wuraren ibada

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu

Gwamnan Legas ya bude wuraren ibada

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ba da umarnin bude masallatai da coci-coci a Jihar daga ranar bakwai ga watan Agusta.

Gwamnan ya kara da cewa sassaucin ya shafi masallatan Juma’a ne da ibadar coci a ranar Lahadi kadai.

Gwamna Sanwo-Olu ya sanar cewa daga Juma’a 7 ga watan Agusta za a bude masallatan Juma’a sannan a bude coci-coci a ranar Lahadi tara ga wata.

A jawabinsa ga ‘yan jarida a gidan jihar, gwamnan ya ce an kara yawan mutanen da za su iya taruwa a wuri guda daga mutum 20 zuwa 50.

Jihar Legas ita ce cibiyar cutar coronavirus ta sanar da shirin bude wuraren ibada amma ta dage matakin saboda karuwar masu cutar.