✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Legas ya mika mulki kasa da awa 24 na ranar mika mulkin

Gwamnan Legas mai barin gado Akinwumi Ambode ya mika mulki ga zababban gwamnan jihar Mista Babajide Sanwo-Olu tare da mataimakin sa kasa da awa 24…

Gwamnan Legas mai barin gado Akinwumi Ambode ya mika mulki ga zababban gwamnan jihar Mista Babajide Sanwo-Olu tare da mataimakin sa kasa da awa 24 da lokacin da aka ware domin yin haka wato ranar 29 ga watan Mayu 2019.

Gwamna Ambode ya miqa mulkin ga sabon Gwamnan na Legas a wani taro da ya yi da shi a gidan gwamnatin jihar da ke Allausa a Ikeja a yau Talata.

Sabon Gwamnan jihar Mista Babajide ya shaida wa ‘yan jaridu cewa gwamna Ambode ya mika masa mahinmman takardu dauke da bayanan mulki da nasarorin sa ya kuma ba shi shawarwari.