Da Dumi Dumi

Gwamnan Nasarawa ya karrama ’yan kwallon jihar

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Alhaji Sule
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Alhaji Sule

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Alhaji Sule ya saka wa ’yan wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta mata ta jihar  da ake kira Amazon da Kungiyar Kwallon Kafa ta maza ta Nasarawa United dangane da nasarorin da suka samu.

Kungiyar Amazon ta lashe Kofin Kalubale (Aiteo Cup) na kasa da aka yi a Kaduna yayin da ita Kungiyar Nasarawa United ta samu lashe Kofin Gasar AHLAN 2019 da ya gudana a birnin Kano.

A wata kwarya-kwaryar liyafa da Gwamnan ya shirya wa zakarun ’yan wasan a garin Lafiya, ya bai wa shugabannin kowace kungiya kyautar Naira miliyan biyu, yayin da ya ’yan wasan kungiyoyin biyu kyautar Naira miliyan biyar ga kowace kungiya. Su kuma kungiyoyin magoya bayan kungiyoyin sun samu kyaututtukan Naira miliyan daya.

Da yake karin bayani Gwamnan ya ce nasarorin da kungiyoyin suka samu a bana yana nuni da wata alama ta samun ci gaba a harkokin wasanni a jihar.

Ya ce, “Ina son in mika sakon taya murna ga wadannan kungiyoyi bisa nasarorin da suka samu a matakin kasa. Kuma ina tabbatar muku cewa wannan gwamnatin tamu tana ba harkokin wasanni muhimmanci.

ADVERTISEMENT

Gwamnatina tana kokarin ganin ta zakulo duk wasu masu basira ta tallafa musu tare da ba su damar su nuna irin basirar da Allah Ya ba su domin ta haka ne za mu iya rage zaman kashe wando a tsakanin matasanmu, tare da samar wa matasa ayyukan yi a fadin jiharmu.

Don haka, muna da burin farfado da makarantar horar da wasanni ta jiha don bai wa masu basirar damar samun horon da ya kamata.”

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya