✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Neja ya ce yana nan daram a sabuwar PDP

Gwamnan Jihar Neja Dokta Aliyu Babangida ya musanta rahoton da jaridar Daily Trust ta ranar Talatar da gabata ta buga cewa yana yunkurin ficewa daga…

Gwamnan Jihar Neja Dokta Aliyu Babangida ya musanta rahoton da jaridar Daily Trust ta ranar Talatar da gabata ta buga cewa yana yunkurin ficewa daga sabuwar PDP, Gwamnan ya ce shi ne shugaban Gwamnoni 7 da ake kira lakabin G-7 da ke adawa da shugabancin Bamanga Tukur.
A ranar Talatar Daily Trust ta buga labarin cewa wata majiya ta ce Gwamnan na shirin barin sabuwar PDP ba tare da ta ambaci majiyar ba. A labarin majiyar ta ce Gwamnan ya zabi ya dawo PDP da Bamanga Tukur ke shugabanci.
Sakamakon karyata rahoton da Gwamnan ya yi cewa jaridar Daily Trust ta buga labarin da ba shi da tushe balle makama, ya sanya jaridar ta bayyana cewa ta samu wancan labari ne daga Mai taimaka wa Gwamnan kan Harkokin Watsa Labarai danladi Ndayebo ne, inda ta ce ya bayyana wa wakilinta hakan a ranar Litinin da daddare sannan ya amince a buga labarin cewa Gwamnan zai balle daga Gwamnoni Bakwai masu adawa da shugabancin Bamanga, ya kuma bar sabuwar PDP.
Jaridar ta buga labarin ne bisa ga sahihanci majiyar saboda Mai taimaka wa Gwamnan ba zai bayar da labarin ba tare da amincewar Gwamnan ba.
Ndayebo ya shaida wa wakilinmu cewa Gwamnan Jihar Neja Dokta Babangida Aliyu zai balle daga sabuwar PDP sakamakon matsin lambar da yake samu daga jiga-jigan jam’iyyar, kuma zai fice ne domin idan ya ci gaba da zama a sabuwar PDP zai rasa iko da jam’iyyar a jiharsa. Mai magana da yawun Gwamnan ya ce Gwamnan ya samu matsin lamba daga Shugaban Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP na kasa, Cif Tony Anenih da Cif Raymond Dokpesi da tsohon Darakta-Janar na Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) Mista Ben Bruce, wadanda suka gana da shi a lokuta mabambanta suka nemi ya dawo PDP karkashin Bamanga.
Gwamna wanda ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar Ma’aikata ta kasa a Minna a ranar Talata ya ce labarin da Daily Trust ta buga aiki ne na makiya da suke neman farraka hadin kan Gwamnoni Bakwai masu adawa da shugabancin Bamanga.
Ya ce: “Na kadu matuka da na tashi a safiyar nan (Talata) na karanta rahoton wata jarida da idan tana neman karin bayani a wurina kai-tsaye take kirana amma don ina wata ganawa sai kawai suka shiga cikin gari suna baza labarin zan balle daga cikin Gwamnoni Bakwai.
“Maganar gaskiya ita ce har yanzu Babangida Aliyu mamba ne a sabuwar PDP, kai ni ne jagoransu. Don haka na dauki wannan labarin a matsayin aikin makiya ne. Sun kirkiri wannan labarin ne don sun farraka hadin kanmu, bayan kuma babu wani abu makamancin hakan. Na ga hannun wadansu daga cikin wadanda suka kitsa wannan labarin.  Don haka ina fata jama’a za su yi fatali da ire-iren wadannan labarai da suke karantawa a cikin jaridu, domin akan kirkire su ne don wata mummunar manufa,” inji Gwamnan.
Gwamnan ya ce ba haka kawai ya sanya bai halarci taron Gwamnoni Bakwai ba, hakan ya faru ne sakamakon canja lokacin taron da aka yi, baya ga haka ba ya da cikakkiyar lafiya, kuma ya sanar da uku daga cikin gwamnonin halin da yake ciki, sannan ya ba su hakuri, amma sai ga shi rashin halartarsa ya tayar da kura har ana cewa zai balle daga sabuwar PDP.
“A wannan ranar na tsara ba zan bar Minna ba sai karfe 2:00 na rana don an riga an ce za a yi taron da karfe 8:00 na dare, ana cikin haka sai aka kira ni aka sanar da ni cewa Gwamnan Sakkwato ya nemi a dawo da taron karfe 2:00 na rana saboda yana da bikin bude jami’ar jihar da zai yi washegari a Sakkwato. Hakan ya sanya na ba su hakuri domin babu yadda zan iya samun taron tunda a lokacin ina Minna. Na yi magana da uku daga cikinsu na kuma nemi su ba da uzurina, musamman da ba ni da cikakkiyar lafiya. Kada a manta idan sauran ’yan uwana gwamnoni ba sa nan, nakan halarci taro a madadinsu, don haka ban ga dalilin da zai sa don ban halarci taron ba, sai a murda batun ya koma cewa zan balle daga cikin gwamnoni bakwai din,” inji Aliyu.
Ya ce: “Ba wannan ne lokaci mafi dacewa da mutum zai yanke hukuncin ballewa ba. Ba zai taba yiwuwa rana tsaka ka ce ka balle daga wani bangare ba bayan kuma ana ci gaba da tattaunawa. Ba yadda za a yi mutum ya balle a wannan lokaci. Lokacin yanke hukunci zai zo ne bayan mun kammala tattaunawa da Shugaban kasa.
“Bayan mun kai karshen tattaunawarmu idan matsayar da aka cimma ta yi wa mutum sai ya tsaya, haka wadanda matsayar ba ta yi musu ba sai su kama gabansu. Amma ina so a sani duk hukunci da kowane bangare ya dauka dukkanmu ’yan Najeriya ne.”

 

… Muna nan kan labarinmu

An jawo hankalinmu sakamakon musanta babban labarin jaridarmu ta Daily Trust ta ranar 29 ga watan Oktoba, 2013 mai taken ‘Gwamna Aliyu zai valle daga sabuwar PDP.’ Gwamna Babangida Aliyu da kuma mai magana da yawunsa Mista Xanladi Ndayebo sun musunta batun vallewar.
Wannan musantawar ta ba mu mamaki domin shi da kansa mai magana da yawun Gwamnan ya kira wakilinmu ya sanar da shi yunqurin vallewar Gwamnan. Mun yi matuqar kaxuwa da mai magana da yawun Gwamnan ya musanta labarin da shi ne ya samar da shi.
Abu ne marar daxi mu bayyana majiyar da ta ba mu labari, domin muna da masaniyar qa’idar aikin jaridar da ta bayyana xan jarida zai iya tafiya gidan yari don ya asirta majiyar da ya samu labarinsa.
Mun karanta labaran da aka xaure ’yan jarida don sun qi bayyana majiyar da suka samu labaransu a sassan duniya. Sai dai bambanci da ke akwai a nan, shi ne bai kamata majiyar labari ta yi qoqarin tanqwara kafar labarai da kuma wasa da hankalinn jama’a ba, saboda wani dalili das hi ko ita suka sani.
Babban Edita.