Aminiya

Gwamnan Ogun ya nuna takaici kan rasuwar dalibai da motar Kwastam ta kade

Gwamnan Jihar Ogun Yarima Dapo Abiodun ya bayyana takaici kan yadda hadarin motar da ya shafi jami’an Hukumar  Kwastam ya yi sanadiyar rasuwar dalibin wata makarantar sakandare tare da jikkata wadansu ’yan makarantar

A wata sanarwa da Sakataren Watsa Labaran Gwamnan, Mista Kunle Somorin ya fitar ta ce gwamnatin ba za ta lamunci kisan ’ya’yan jihar ba da sunan yaki da ’yan fasakwauri. Sanarwar ta ce Gwamnan ya kadu da jin labarin rasuwar daliban Makarantar Ijumo da ke Ihunbo a yankin Ipokiya, ta ce gwamnatin za ta yi bincike domin bin didigin yadda lamarin ya auku.

ADVERTISEMENT

A bangaren Hukumar Kwastam ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda lamarin ya rutsa da daliban sai dai ta ce ba dalibai uku ne suka rasu a hadarin ba kamar yadda ake yayatawa. Shugaban Hukumar  Kwastam ta Shiyya ta Daya da ke Jihar Ogun, Mista Michael Agbara ya ce ba kamar yadda ke yayatawa a kafafen sadarwa cewa jami’an hukumar sun yi harbi a kan daliban, “Ba harbi ko bin ’yan fasakwauri ne ya haddasa lamarin ba, wannan abu hadari ne da ya rutsa da daliban kuma dalibi daya ne ya rasu mai suna Opeyemi Odusinan yayin da zuwa yanzu an sallami dalibai  biyu  daga asibiti, wani Sunday Adeniyi na ci gaba da jinya a babban asibitin gwamnati da ke Idiroko. Ko a safiyar yau mun ziyarce su muna ci gaba da tattaunawa da iyalin mamacin da wadanda suka jikkata za mu daukin nauyin kudin maganinsu,” inji shi.

Ya ce hadarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata bayan da jami’an hukumar suka kwato wata motar fasakwauri a yankin, “Jami’anmu sun yi nasarar kwato motar sun tuko ta daga cikin daji zuwa bakin hanya a yankin na Ihunbo a nan ne suka hango wani mai babur dauke da mace mai ciki, kuma a yunkurin kauce wa mai babur din ne sai motar ta kwace wa direban inda ya auka wa daliban da ke gefen hanya,” inji shi

ADVERTISEMENT