✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Sakkwato zai tallafa wa ’yan kasuwa da bashi

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar gane wa ido a Kamfanin Sarrafa Roba na ANHAS da ke Modorawa a Karamar Hukumar…

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar gane wa ido a Kamfanin Sarrafa Roba na ANHAS da ke Modorawa a Karamar Hukumar Wamakko.

A lokacin ziyarar, Gwamnan ya jinjina wa wanda ya kafa kamfanin, Alhaji Nura dan asalin Jihar Sakkwato, kan kokarin da ya yi na kawo wannan ci gaba. Ya ce wannan ba karamin taimakawa zai yi ba wurin samar wa matasan yankin ayyukan yi.

Kan korafin da mai kamfanin ya yi na bukatar fili don fadada kamfanin nasa, Gwamna Tambuwal ya ce zai ba Kwamishinan Filaye umarnin a ba shi fili kyauta ba tare da ya biya ko sisi ba. Zai kuma amfana da bashin Naira miliyan 50, inda zai biya sau uku. Ya ce wannan tsari zai ci gaba da gudana ga ’yan kasuwar jihar, a rika ba su rancen kudi suna biya cikin shekara uku, don bunkasa kasuwancinsu.

Gwamnan ya shawarce shi da ya hada hannu da wadansu ’yan kasuwa, su saka hannun jari a kamfanin domin ya dore. Ya kuma yi kira ga ma’aikatan da ke wurin su rike aikinsu da muhimmanci, don ci gaba da samar da ingantattun abubuwan da ake sarrafawa a wurin.

A  jawabin Kwamishinan Ciniki da Masana’antu, Alhaji Bashir Gidado ya jinjina wa wanda ya kafa kamfanin. Ya ce yin hakan ya kawo saukin zuwa neman wasu abubuwan da ’yan kasuwa ke yi a wasu garuruwa; tunda ga su ana yi cikin garinsu.

Ya ba da tabbacin goyon bayan maaikatarsa da gwamnati ga ’yan kasuwa a koyaushe

Tun farko Alhaji Nura kira ya yi ga gwamanti ta ci gaba da karfafa wa masu masana’antu da ke jihar don bunkasa su. Ya ce kamfaninsa na da kudirin kara kirkiro abubuwan da za su sarrafa domin amfanin al’umma.

Kamfanin shi ne irinsa na farko a jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara kuma yana yin butoci da faka da ludayi da robar cin abinci da sauransu.