Daily Trust Aminiya - Gwamnan Taraba ya raba wa ’yan majalisa jifa-jifai
Subscribe

Gwamnan Taraba ya raba wa ’yan majalisa jifa-jifai

Gwamna Jihar Taraba, Darius Ishaku ya raba wa ’yan Majalisar Dokokin Jihar 24 motocin alfarma na Prado Jeep kirar Shekarar 2020.

Gwamna Darius ya raba wa ‘yan Majalisar motocin ne bayan sun bayyana gamsuwa da kamun ludayin gwamnatinsa da Shugaban Majalisar, Joseph Albasu Kunini a zaman Majalisar na ranar Litinin.

Aminiya ta gano cewa an yi rabon motocin ne rana guda bayan wata kungiya ta yi zargin cewa jam’iyyar APC da ke adawa a jihar na neman ta saye ’yan PDP a Majalisar su sauya sheka zuwa APC.

Kungiyar mai tutiyar kare ’yan Jihar Taraba ta yi zargin cewa APC na neman yin amfani da kudi ta saye ’yan Majalisar su tsige Shugabanta da kuma Gwamna Darius Ishaku.

texem
More Stories