✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Zamfara na dab da dawowa APC  – Yariman Bakura

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Sani Ahmad Yariman Bakura, a ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Sheikh Dahiru Bauchi da iyalan marigayi Abubakar Tafawa Balewa…

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Sani Ahmad Yariman Bakura, a ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Sheikh Dahiru Bauchi da iyalan marigayi Abubakar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi ya amsa tambayoyin manema labarai, inda ya bayyana dalilin da zai tsaya takarar Shugaban Kasa a shekarar 2023:

Ana cewa za ka tsaya takarar Shugaban Kasa a 2023, me za ka ce?

Gaskiya ina sane da wannan magana cewa wadansu mutane a Najeriya suna kira gare ni in tsaya takarar Shugaban Kasa. Na san akwai mutane daga jihohin Kano da Katsina da Kaduna da wasu jihohi da suka hada kansu suka yi kamar wata kungiya kuma na samu labari har sun je gidan rediyon Kano da Kaduna sun gabatar da shirye-shirye don neman in fito neman takara. Ka ji ta inda na fara jin labarin wadannan mutane da ke goyon bayana. Bayan sun yi wadannan shirye-shirye sai suka same ni, sai na tambaye su me ya sa suke yin irin wadannan abubuwa, sai jagoransu Kwamared Ja’afar wanda shi ne shugaban wayar da kan jama’a na Kungiyar Yakin Neman Zaben Buhari/Masari 4+4, ya ce min sun zauna ne a matsayinsu na matasan ’yan siyasa, suka yi nazari a kan ’yan siyasar Arewa da dama daga bisani suka tantance suka ga cewa na fi cancanta su goya mini baya, domin su kira ni in zo in tsaya takarar Shugaban Kasa a 2023. Na ce musu anya ba a yi garaje ba? Kuma a matsayinmu na Musulmi babu wanda ya san gobe sai Allah.Haka muka yi ta tattaunawa har suka nuna min cewa ko a kasar Amurka da zarar an kammala zabubbuka ake fara maganar zabe mai zuwa. To ni ma sai Allah Ya sa na fara jin cewa in Allah Ya nufa zan tsaya neman takarar Shugaban Kasa a zaben 2023.

A wace jam’iyya za ka tsaya ganin ana tunanin Jam’iyyar APC akwai wadansu jiga-jigan ’yan takara?

Duk abin da ya zama jita-jita, ba za ka ce ka yanke ba. Na fara wannan siyasar ce a Jam’iyyar APP a 1998 aka zabe ni a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara daga bisani muka sauya suna zuwa ANPP daga bisani kuma muka yi hadakar ACN da ANPP da sauransu muka kafa APC. Tun shigata siyasa ban taba canja jam’iyya ba kuma na fara siyasa a karkashin Jam’iyyar DPN lokacin marigayi Janar Sani Abacha. Dukkan mukamai da ake takara a kansu Allah Yake yin ikonSa, Ya ba wanda Ya nufa. Ba wanda yake iya bai wa kansa. Yau idan dukkan ’yan Najeriya za su taru su ce Yarima suke so, idan Allah bai nufa ba hakan ba zai taba kasancewa ba. Idan kuma Allah Ya kaddara cewa zan zama zan yi shugabancin kasar nan.Saboda haka ban dauki neman shugabanci a matsayin yaki na a mutu ko a yi rai ba, na dauke shi a matsayin kaddara daga Allah.

Abin da yake wajibi shi ne mutum ya nemi tsayawa takara kuma a matsayina na Musulmi kamar yadda na fadi, ba ni na fara wannan yunkurin ba. Shi dan siyasa babban burinsa shi ne ya zama Shugaban Kasa, ka ga yanzu bayan na yi Gwamna shekara 8, Sanata shekara 8 ba wani mukami da ya rage mini in yi, in ba Mataimakin Shugaban Kasa ko Shugaban Kasa ba. Kuma cikin ikon Allah in har Ya kaddara mini zan nemi kujerar Shugaban Kasa in har muna raye cikin ikon Allah a 2023.

Wadansu mutane suna korafin cewa har yanzu akwai wasu abubuwan da ba su sauya zane ba tun lokacin PDP, me za ka ce?

Kowace gwamnati tana da irin nasarori da kuma irin matsalolin da take cin karo da su, amma abu mafi muhimmanci shi ne nasarorinta su dara matsalolin. A gaskiya tsakanina da Allah da Ya halicce ni Shugaba Buhari yana yin iyakacin kokarinsa. Ka ga yanzu mutane ba sa yin tururuwa su dauki dukiyoyin gwamnati suna wadaka da su a fili yadda suka ga dama kamar yadda suke yi da a karkashin mulkin PDP. Sai dai kawai abin da nake son gani a karkashin wannan gwamnati shi ne a mayar da hankali wajen yakar talauci a cikin al’umma. Ka ga hanya mafi sauki da za ka magance matsalar rashin tsaro ita ce ka kawar da talauci. Idan har mutane suna da ayyukan yi kuma aka karfafe su za su fi mayar da hankalinsu wajen yin san’a’oinsu, kuma hakan zai magance matsalar tsaro. Saboda haka idan Fadar Shugaban Kasa za ta mayar da hankalinta da tsare-tsaren tatalin arziki kan kawar da talauci, ta fuskanci noma da ilimi, al’amura za su sauya a kasar nan.

Akwai rade-radin cewa kuna zarwacin Gwamna Matawalle ya koma APC?

Kamar yadda na fada Allah Yake bada mulki ga wanda Ya so. Shi Mai girma Gwamnan Jihar Zamfara na yanzu da can a baya ya rike min mukamin Kwamishina, tun farko muna tare da shi cikin jam’iyya daya tun 1998, har zuwa 2011 lokacin shi da tsohon Gwamnan Jihar Abdul’aziz Yari su abokai ne, kuma abokan aiki ne lokacin da Yari yake shugabancin jami’yyarmu. Saboda sabanin da suka samu lokacin zaben fidda gwani sai suka bar jam’iyyar tare da tsohon Mataimakina da ma wadansu ’yan jam’iyyar suka koma PDP. In kun tuna a zaben da ya wuce APC ta yanke shawarar  yin zaben fidda gwani kai-tsaye wato ta hanyar kato-bayan-kato tun daga mazaba. Saboda wasu dalilan ba a samu damar yi ba, mun yi zabe mun lashe mun kuma yi iyakacin kokarinmu a matsayinmu na jagororin jam’iyya amma Allah Ya nufa zai zama Gwamna. Mun tsayar da ’yan takara tun daga majalisa har zuwa Gwamna kuma sun ci zabe, amma saboda ba mu yi zaben fidda gwani kamar yadda tsari da dokokin jam’iyyarmu suka tsara ba, Kotun Koli ta rusa.Wanda Allah Ya nufa shi zai zama Gwamna kuma Allah Ya ba shi.Amma nan ba da dadewa ba dama mu iyali daya ne, kuma za mu dunkule mu dawo gidanmu guda daya. Gwamna dan gidanmu ne tun daga APP da ANPP kamar yadda na fadi rashin jituwa ya faru ya sa wadansu mutanenmu suka koma PDP, kuma nan bada dadewa za ka ga mun dunkule waje guda, muna kan magana da juna.

Za ku kira Gwamna ya koma APC ke nan?

Ba sai mun kira shi ba, shi ma ya sani zai dawo gidansu. Kusan ’yan APC ne cikin PDP a Zamfara don haka gidanmu guda ne. Don haka muna kan tattaunawa da juna.

Idan har ka samu nasara me za ka yi?

Zan yaki talauci, kuma zan sa farin ciki a  zukatan mutane. Zan yi aiki tukuru wajen bunkasa harkar noma kuma muna rokon al’umma su kara hakuri su kara yawaita addu’a Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya Ya kawo ci gaban kasa baki daya.