✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gwamnati ba ta ce gwamnoni su boye kayan tallafi a rumbuna ba’

Gwamnoni ne suka yi gaban kansu suka boye kayan tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ba su

Gwamnatin Tarayya nesanta kanta da gwamnoni da Ministan Birnin Tarayya da suka jibge kayan tallafin da ta raba musu na rage radadin annobar COVID-19 da suka ki raba wa jama’a ba.

Wata majiya a Kwamitin Rabon Kayan Tallafin ga jihohi ce ta tabbatarwa da Aminiya cewa ba Gwamnatin Tarayya ce ta ce gwamnonin su ajiye kayan ba.

Tun ranar Larabar makon jiya ne dai mutane a jihohi ke ta fakewa da zanga-zangar #EndSARS suna fasa rumbunan ajiyar kayan a jihohinsu suna kwashe kayan abincin da duk abin da idanunsu suka yi arba da shi.

Hakan dai ya sa jihohi da dama kokarin kawo dalilan abin da ya hana su raba wa al’ummar jihohinsu tallafin tun a wancan lokacin.

Ya zuwa yanzu dai Fadar Shugaban Kasa da Ma’aikatar Jinkai da Agajin Gagggawa sun ki cewa uffan kan ko gwamnonin jihohi sun boye kayan ne da gangan ko kuma a’a.

A baya dai mutane da dama sun yi ta zargin gwamnatin tarayya kan batun rabon kayan da ta ce ta rabawa jihohin.