✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ba ta cika mana alkawarin cin kofin matasa na Duniya na 1985 ba -Koci Bala Shamaki

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets da ya lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1985 Bala Shamaki ya koka akan yadda tun bayan…

Koci Bala ShamakiKocin kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets da ya lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1985 Bala Shamaki ya koka akan yadda tun bayan da suka lashe gasar a wancan lokaci har yau gwamnatin tarayya ba ta cika alkawarin da ta yi musu ba.

Koci Bala Shamaki ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a garin Minna da ke Jihar Neja.
Kocin ya nuna damuwarsa a kan yau kimanin shekara 28 da wancan alkawari amma har yanzu ba a cika musu ba.
“A halin yanzu ina cikin kuncin rayuwa saboda shekaruna sun fara nisa kuma ga shi ba ni da abin hannu don haka nake roko gwamnati ta yi wa Allah ta cika alkawarin da ta yi mana a lokacin da muka lashe kofin duniya na matasa a karon farko a shekarar 1985.
Kocin ya ce abin mamaki ne ganin wadanda suka biyo bayansu an biya su hakkokinsu a kan kari amma har yanzu abin bai zo gare su ba.
Daga nan kocin ya jinjina wa ’yan kwallon kafa na Golden Eaglets da suka lashe kofin duniya karo na hudu a Dubai. Ya yi kira ga gwmanati da ta yi duk mai yiwuwa ta ga ta cigaba da horar da matasan don su maye gurbin matakin manya a nan gaba.
Ya ce “na yi farin cikin ganin daya daga cikin mataimakan kocin mai suna Nduka Ugbade a lokacin da nake horar da su shi ne kyaftin din kungiyar a shekarar 1985 sannan yanzu ya kasance mataimakin koci ga Manu Garba, lallai na yi alfahari da hakan, don ya dage kofi a matsayin dan wasa a wancan lokaci, yau kuma ya daga a matsayinsa na mataimakin koci.
Koci Bala Shamaki ya ce ko yanzu gwamnati ta nemi ya yi mata aiki a matsayin koci zai amsa gayyata don yana yi ne saboda kishin kasa ba don abin da zai samu kadai ba.