✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ba ta cin nasara sai da taimakon malaman gona – Kwamishinan Gona

Kwamashinan Aikin Gona na Jahar Jigawa Alhaji Kabiru Ali kuma ya dauki alkawarin dawo da malaman gona cikin hayyacinsu tare da samar da takin zamanin…

Kwamashinan Aikin Gona na Jahar Jigawa Alhaji Kabiru Ali kuma ya dauki alkawarin dawo da malaman gona cikin hayyacinsu tare da samar da takin zamanin da ya dace da irin kasar noman jahar domin amfanin manoman jahar. Kwamishinan ya fadi haka ne a wata ganawa da ya yi da wakilinmu a makon da ya gabata. Ga yadda hirar ta gudana kamar haka:

 

Aminiya: Ranka ya dade masu karatu za su so sanin sunanka da matsayinka a halin yanzu.

Kwamishina: Sunana Kabiru Ali tsohon kwamashinan aikin gona kuma tsohon manajan kamfanin JARDA masani akan harkar kwari tsohon baturen gona tun zamanin turawa, tun Jahar Jigawa ta na tsohuwar Jahar Kano. Sannan tsohon babban sakatare a hukumar aikin gona ta jigawa kuma tsohon shugaban ma’aikatan Jahar Jigawa wadda na yi ritaya sabuwar gwamnatin jigawa karkashin jagorancin gwamna mai ci alhaji Badaru Abubakar ta sake daukoni ta bani matsayin kwamashinan aikin gona a halin yanzu, saboda in bada gudumawata akan harkar aikin gona a jahar nan.

Aminiya: Wacce matsala ce ta fi damun ma’aikatar gona ta Jahar Jigawa a halin yanzu, kuma ya ya za a magance ta?

Kwamishina: Na bar ma’aikatar aikin gona da ma’aikata wadatattu wadda a kalla malamin gona yana iya duba mutun dubu sabanin yanzu da malamin gona zai duba manoma 1,600 wadda hakan ya sabawa ka’idar aikin malaman gona. Na fuskanci malaman gona su na cikin wani hali na karancin malaman kuma ba su da kayan aiki da suke duba manoma. Saboda haka za mu dawo da martabar malaman gona kuma zamu kara yawan malaman gona a jahar a kokarin gwamnatin jahar na inganta tsarin aikin gona da tallafawa manoma a jahar nan.

Ni wannan kujerar ta kwamashinan aikin gona ba bakuwa ce a wajena ba, domin a baya na taba hawanta sai dai kawai in ce yanzu na ga akwai canji mai yawa sabanin yadda na bar ma’aikatar gona a baya. A lokacin da na bar ta ta na da isassun ma’aikata da suke duba manoman da ake da bukata, amma yanzu akwai karancin malaman gona a jahar hakazalika baburan da muka rabawa malaman gonar babu su, sun mutu. Da na bincika sai na ga saboda karancin malaman gona da hukumar aikin gona da jahar ta ke da su yasa ta rage yadda take tafiyar da ayyukanta.

Sannan ita kanta JARDA tun da aka gina ta yau shekaru goma sha bakwai, amma ba a taba yi mata ko da fanti ba, banda warin rima da lalacewa ba ta da komai, amma cikin ikon Allah za mu gyara ta kuma za a dawo da Agency allowance don karfafa wa malaman gona gwiwarsu, su tsaya akan aikinsu saboda babu wata nasara da gwamnati za ta iya samu sai da taimakon malaman gona, idan aka yi la’akari da mahimmancinsu a wajen manoma.

Aminiya: Da yake na gano akwai matsalar malaman gona, ko akwai wani tanadi da gwamnati ta yi na magance matsalar?

Kwamishina: Gaskiya ne za mu yi bakin kokarinmu wajen dawo da martabar malaman aikin gona ta hanyar kara yawan malaman gona a jahar. A kasar Indiya malamin gona zai iya Cuba manomi dubu. Yanzu haka gwamnatin Jaha Jigawa ta ba mu malaman gona 159 da su ke karkashin kulawar kananan hukumomin jahar 27 mu na ba su horo akan aikin gona. Su zama malaman gona su rika fadakar da manoma da kuma ba su shawara. Idan sun kammala za mu sayi babura 350 mu ba su domin daukar bayanan manoma da ba su shawarwari, da zarar mun kai ga haka komai zai koma kan hanyarsa ta da.

Aminiya: Shin manoma a Jigawa sun sami taki da sauki a bana?

Kwamishina: Ai zagaya wa zaka yi ka gani, manoma babu abin da za su ce da gwamnati sai godiya duk da cewar an dan yi karancin takin a bana, amma saboda mu a Jigawa mun yi abin cikin tsari, mun ba da takin ta hannun ‘yan kwamiti shi yasa takin ya isa wajen manoma a lokaçin da su ke da bukatarsa. Kuma batun sayar da da takin ta wayar salula mu ba mu amince da tsarin ba, domin wasu ‘yan kasuwa ne dake amfani da wanan damar su ke cutar manoma ba su samun takin akan lokacin da su ke da bukatar takin. Gwamnati ta yi tanadin duk hanyoyin da ta bi na zahiri a wajen baiwa manoma takin a daminar badi don hana macuta sace takin da ya kamata manoman su samu.