✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ba ta damu da mu ba – Shehun Bama

Garin Bama da ke Jihar Borno ya sha fuskantar hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka masu yawa. Na baya-bayan nan…

Garin Bama da ke Jihar Borno ya sha fuskantar hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka masu yawa. Na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai ranar 18 ga watan Fabrairu. Maharan kungiyar Boko Haram sun kai hari garin, inda suka kashe kimanin mutane 100, suka kuma kona gidaje fiye da 1000 da ababan hawa fiye da 400, daga bisani kuma suka banka wa fadar Shehun Bama wuta, a sakamakon harin harkokin kasuwanci sun durkushe a garin. Shehun Bama, Kyari Ibrahim Ibn Elkanemi, wanda ake gani mai kawaici ne da kankan da kai, a wannan karon ya nuna rashin jin dadinsa a kan hare-haren. A hirar da ya yi da Premium Times a fadarsa da aka kona, basaraken ya dora alhakin tabarbarewar tsaro a Jihar Borno a kan gwamnatin tarayya.Ga yadda hirar ta kasance:
Tambaya: Me za kace game da harin da aka kai maka a watan Fabrairu?
Amsa: Da misalin karfe hudu na asuba, wani mai unguwa ya kira ni ya sanar da ni yi cewa wani mutum daga Goni Kurmi ya aika masa da rubuttacen sako ta waya cewa ya ga wani ayarin motoci da ababan hawa sun kamo hanyar Bama.
Nan take sai na kira wani jami’in tsaro kuma na sanar da shi abun da wancan mutum ya sanar da ni. Sai shi ma ya ce ya samu labarin, wani ne daga ‘yan sintirin da ke farautar ‘yan Boko Haram (Cibilian JTF) ya sanar da shi. Duk da jin haka ban yi kasa a gwiwa ba sai na kira wani Manjo da ke wani barikin a nan Bama, shi ma na sanar da shi abun da ke faruwa. Na kuma yi kokarin samun Kwamandan Birged da kuma Kwamandan rundunar tsaro amma na kasa, saboda layin wayoyinsu ba ya tafiya. Bayan kamar mintuna 30, sai wani mutum ya kira ni ya sanar da ni cewa maharan sun fara cinna wa gidajen da ke wajen garin Bama wuta, sannan suka nufo cikin gari.
Daga nan sai jama’a suka fara yin ta kansu, sai muka fara jin karar bindiga. Jin kadan sai na fahimci harabar fadar ta zama ba masaka tsinke saboda dandazon mata da kananan yara da suka guje wa gidajensu. A daidai lokacin da muke kokarin bude musu kyauren fadar,  ashe maharan sun rigaya ma sun iso fadar, da suka ga cewa mata ne da kananan yara, sai suka umarce su da su bace daga fadar, nan take maharan suka ci gaba da habe-habensu don su watsa mutanen. Bayan kowa ya yi ta kansa, sai suka nufi kyauren fadar, inda a nan take suka tada abubuwa masu fashewa a jikin kyauren don samun hanyar shigowa. Da suka shigo ciki, sai suka zabi wadansu daga cikin motocin da nake amfani da su, kafin su sa wa fadar wuta.Sun sa wa komai a fadar wuta, ciki har da babban ginin fadar da ofis dina da babban dakin taro. Sun kuma kosa motocin guda 30 da suka samu a cikin fadar. Haka  dai suka yi ta kone-kone da harbe-habe, ba su bar garin ba har sai bayan kamar karfe 12 na rana, ka ga ke nan sun kwashe kamar sa’a takwas. Daga nan sai muka fara jin kukan jirgin sama na soji mai saukar ungulu yana shawagi a sama.
Tamabaya: Mutane nawa ne suka rasa rayukansu?
Amsa: Mun yi ta kokarin ganin mun tattara gawanwakin a wuri guda don mu sallace su gaba daya a nan fada gabanin binne su, amma ga alama sakon namu bai isa ga kowa ba, saboda yawancin gawarwakin an binne su ba tare da bata lokaci ba. Amma na san a babban masallacin garin Bama da yake kusa da fadata mun binne gawanwaki 34. Bayan haka kuma an binne wadansu masu yawa. Jama’ata sun kadu ganin yadda aka yi rugu-rugu da fadata, har sai da kura ta lafa na fito bainar jama’a don sallatar mamatan 34, sannan ne suka fahimci cewa na tsira daga harin.
Tambaya: Ya aka yi ka tsira daga harin?
Amsa: Saboda da dalilan tsaro bai kamata na bayyana yadda aka yi ba. Amma iko ne na Ubangiji da kuma taimakon jami’an tsaro da ke tare da ni.
Tambaya: Yaya za ka kwatanta girman harin da asarar da kuma  aka yi?
Amsa: Harin abun takaici ne kuma abun bakin ciki ne. Garin Bama shi ke da kasuwar da tafi kowace a Jihar Borno, kamar yadda aka sani, gari ne na kasuwanci saboda yadda ya yi iyaka da kasar Kamaru. Amma biyo bayan harin ‘yan Boko Haram harkokin kasuwancin sun durkushe gaba daya.
Tambaya: Yaya girmar asarar?
Amsa: Muna ci gaba da tattara alkaluma amma ka sani cewa asarar da harin ya jawo mai yawa ce. Amma Shugaban garejin motoci na garin ya bayyana min cewa a cikin gareji hudu da aka kai harin, an kona motoci 116 kurmus. Wannan ana maganar motocin da ake haya da su ne. Idan muka tabo bangaran motocin jama’a kuma, babu wani gida da maharan suka ziyarta ba tare da cinna wa motocin gidan wuta ba. In takaita maka zancen, hatta babur din nan mai kafa uku (Keke-Napep) bai tsira daga gare su ba. Wannan abun takaici ne.
Tambaya: Wane irin dauki kuka samu daga jami’an tsaro?
Amsa: Zan iya cewa jami’an tsaro sun yi iyakar kokarinsu. Amma idan za a dora su bisa mizani, zan ce ba su yi abun a yaba ba, ba ko saboda sun gaza ba, sai don saboda ba su da isassun makaman da za su tunkari ‘yan Boko Haram. Sojojinmu na amfani ne da bindiga samfurin AK-47, su kuwa maharan na rike ne da samfarin RPG da sauran manyan makamai.
Tambaya: Wane kira za ka yi ga gwamnatin tarrayya?
Amsa: Kira na ga dukkan shugabannin shi ne su yi kokarin sauke nauyin da ke kawunansu. Saboda a sakamakon wannan hare-haren mutane sun daina neman tamakon gwamnati, sun koma ga Allah. Amma wannan lokaci ne na tsage gaskiya, kuma gaskiyar ita ce gwamnati ta gaza. Duk shugaban da ya yi watsi da bukatar jama’arsa ya kiyayi ranar da tura za ta kai bango.
A yanzu dai  babu wani aminci da yarda da za a ce mutane ke da shi kan shugaban kasa ko gwamna  ko shugaban karamar hukuma, kai hatta mu masu rike da sarauta, saboda gwamnatin ta kasa, Zan kara nanatawa, babu wani amince da yarda da jama’armu ke da ita, daga kan shugaban kasa zuwa shugaban karamar hukuma.
Zan yi wannan kira zuwa shugaban kasa da gwamnoni da kuma shugabannin kananan hukumomi cewa su ji tsoran Allah. Ku kum masu yada labarai ku dage a kan fadin gaskiya, duk da cewa gaskiya daci gare ta. ‘Yan jarida ku daina kallon batun kamar wata dama ce tattara labarai don neman suna. Matsalar ta shafi kowa, saboda haka a daina sa son rai ko siyasa ko neman abun duniya, babu wanda ya tsiya daga matsalar.
Gwamnati ta gaza; ta kasa tsare kowa da komai, ba na  shayin fadin haka. Saboda kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora mata alhakin kare rayuka amma babu rayukan da ta kare a nan. Abun mamakin a nan shi ne, idan da wannan tashin hankalin na faruwa ne  a wani bangare na kasar nan da ba za a yi watanni shida ba tare da an ruguza kasar gaba daya ba, saboda yadda su ‘yan wancan yankin ke kallon al’amura. Na san cewa idan da a can ne wannan ke faruwa, to da gwamnatin Nageriya za ta yi  abun da ya dara wanda take yi yanzu. A yanzu mun fahimci cewa saboda dabi’armu ta kawaici shi ya sa ba a kulawa da halin da muke ciki.
Tambaya: Me kake ganin ya dace a yi cikin gaggawa?
Amsa: Idan gwamnati na so ta kawo karshen matsalar to ya kamata ne ta fara tattara bayanan matsalar daga kasa kuma ta daina dogaro da duk wani irin rahoton tsaro da ake ba ta daga ofis. Su tuntube mu mu da muke yankin, saboda  mu ke da sahihin bayanan tsaro. Amma abun takaici shi ne, abun ya yi kama da hadin bakin mahukunta, duk hanyoyin sadarwa ba sa aiki, tun daga lokacin da aka kai harin har zuwa yanzu, kamar mu ba a Najeriya muke ba. Muna kira  ga gwamnati da ta maido da hanyoyin sadarwa a duk lungu da sakon kasar nan, saboda duk wanda ke  da muhimman bayanai zai iya sanar da mahukunta ba tare da wahala ba.
Ko shakka babu maharan sun kafa sansaninsu a dazuzzukan da ke cikin Jihar Borno amma jami’an tsaro sun kasa cin musu. Sannan babban abun takaicin shi ne, sojojin na karya gwiwar matasa masu farautar ‘yan Boko Haram ( Cibilian JTF) duk sanda suke son su nufi can don farautar ‘yan kungiyar.
Ina da shawara da zan ba gwamnatin tarayya amma ba zan iya fadan ta haka a sarari ba. Idan  da gaske take kuma tana karbar shawara, to a shirye nake na ba ta a kebe. Kuma zan bayyana karara ba tare da jin tsoro ba cewa ina goyan bayan kalaman da Gwamna Borno ya yi kwanakin baya a Abuja kan halin tsaron da ake ciki a Jihar da ma Najeriya baki daya. A ganina, kalaman gwamnan ba su yi zafi ba, saboda bai fadi rabin abun da ke faruwa ba. Wadansu daga Abuja bai kamata su fadi maganganun da za su bata mana rai ba, saboda su gyara siyasar ubangidansu. Akwai mamaki idan ka ga mutumin da bai taba zuwa Kano ba, amma yana zaune daga Abuja ya dunga fadin abun da bai da masaniya a kai. Idan mutum na so ya yi magana a kan yanayin rashin tsaron jihar Borno da yankin Arewa-Maso-Gabas, kamata ya yi ya tare a can domin ya gane wa idanunsa abun da ke faruwa kafin ya fara sharhi a kai.