✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ba ta shirya wa noman auduga ba – Abbas Nabingi

Wani babban manomin auduga a Jihar Gombe, Alhaji Abbas Umar Nabingi, ya ce noman auduga gadon gidansu ne fiye da shekara 40 kuma har yanzu…

Wani babban manomin auduga a Jihar Gombe, Alhaji Abbas Umar Nabingi, ya ce noman auduga gadon gidansu ne fiye da shekara 40 kuma har yanzu ba su bar shi ba; inda shi yake noma kadada 50 na auduga.

Alhaji Abbas Nabingi, ya ce a shekarun baya a gidansu baya ga noman auduga suna gurza ta amma yanzu noman auduga a Najeriya ya mutu kuma gwamnati ba ta shirya farfado da harkar ba.

Ya ce babbar matsalar ita ce idan aka noma wane ne zai saya? Idan za a saya kuma za a saye ta ce da karamin farashi ganin tana da dawainiyya da yawa.

Alhaji Nabingi, ya ce bayan ba ta da farashi a Gombe babu irin angurya mai kya domin irin da ake nomawa shekara da shekaru har yanzu shi ne idan manomi ya noma faduwa yake yi saboda rashin ingancinsa.

“Ya kamata a ce yanzu an samu angurya mai inganci irin wadda ake nomawa a kasar China da sauran kasashe. Amma ba mu samu wannan ci gaba ba tukuna,” inji shi.

Ya ce hatta kaji da ake kiwatawa akwai burolas haka dabbobi, a masara ma akwai iri mai inganci: Amma a auduga an bar su a baya.

Abbas Nabingi, ya ce a bara sun samu wanda ya kawo musu iri mai kyau kadan suka gwada kuma suka samu alherinsa.

Sai ya yi kira ga gwamnati ta kawo musu iri mai inganci idan da gaske tana so ta taimaki manoman auduga. Ya ce abin da ya kara kashe darajar noman auduga a Gombe shi ne rashin tsaro wanda kafin ta gama fasuwa ta nuna makiyaya sun shiga sun cinye audugar.

Manomin ya ce a garin Daben Fulani akwai wani manomi da ya zo ya koka cewa yanzu haka makiyaya sun cinye masa auduga.

Ya ce da za a taimaka wa manoman yadda ya kamata da su kadai a iya gidansu kawai za su noma kadada dubu uku a garinsu na Dasa Hayin Maido kuma a yankin Karamar Hukumar Balanga za su iya noma kadada dubu 30.

Ya ce mutuwar masakun Najeriya ta taimaka wajen kara jefa noman auduga cikin halin kunci.

“Daga shekara 20 zuwa yanzu idan aka noma auduga a Najeriya Indiyawa ne suke zuwa suke saye ta su tafi da ita kuma sai yadda suka ga dama suke saye. Mafita ga noman auduga gwamnati ta tsaya sosai wajen bin hanyoyin da suka dace domin taimaka wa manoma a ga an habaka noman auduga a kasar nan,” inji shi.

Daga nan sai ya ce ya kamata kafin damina ta sauka manomi ya samu iri a hannunsa damina tana sauka ya tafi gona; sannan idan manomi ya noma a saya da farashi mai kyau.