✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati da kungiyoyi su kara shigowa a tallafi karatun ’ya’ya mata –  Sa’adatu  Ka’oje

Malama Sa’adatu Muhammad Ka’oje  mace ce mai kokarin ganin yara maza da mata sun samu ci gaba a rayuwarsu, a kan haka ne take cikin…

Malama Sa’adatu Muhammad Ka’oje  mace ce mai kokarin ganin yara maza da mata sun samu ci gaba a rayuwarsu, a kan haka ne take cikin kungiyoyin koyar da sana’a da dogaro da kai da gyaran tarbiyya a tsakanin ’yan mata da zawarawa. Aminiya ta tattauna da ita kan abubuwan da suka shafi rayuwarta:

Tarihina

Sunana Sa’adatu Muhammad Ka’oje an haife ni a 1972 a Unguwar Titin Koko a Sakkwato. Na yi karatun firamere a Makarantar Model da ke kan titin Birnin Kebbi wacce a yanzu aka fi sani da Makarantar Kimiyya ta Yakubu Mu’azu. Bayan na kare aka kai ni Kwalejin Tarayya da ke Okigwe a Jihar Imo na fara sakandare a can kafin a mayar da ni Kwalejin Tarayya ta Gusau inda na kammala. Na shiga Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari inda na samu takardar shaidar ilimi ta kasa (NCE). Daga nan na wuce Jami’ar Usman Dan Fodiyo duk a Sakkwato na samu shaidar digiri na farko, bayan na kammala ne na fara aiki da makarantu masu zaman kansu daga nan na samu aikin malanta a makarantun gwamnati ina tare da su yau shekara biyar ke nan. Yanzu ni ce Shugabar makarantar Firamare da Karamar Sakandare ta Turaki da ke kan Titin Sarki Yahaya a birnin Sakkwato.

Nasarori

Alhamdulillahi na samu ingantaccen ilimin zamani da na addini. A wurin aikina ba ni da wata matsala da abokan aikina malamai da ma’aikata da dalibai. Daidai gwargwado akwai fahimtar juna a tsakaninmu suna girmama ni ina girmama su mun san mutuncin junanmu kowa ya tsaya matsayinsa tsakaninmu da su sai sam barka. Wannnan halin ne ya sanya makarantar tamu ta samu dimbin nasarori inda take sahun gaba cikin makarantun Jihar Sakkwato. Abin da zai kara fito maka da wannan maganar shi ne yadda aka gyara makarantar sosai yanayinta ya zama mai kyau, yara suka dawo da karatu fiye da kashi 70 cikin 100 sai ka zo makarantar za ka fahimci haka.

Kalubale a rayuwa

Rayuwa tana da sauki komai yakan zo ya tafi, a kowane lokacin gudanar da wani abu na ci gaban rayuwarka kana iya haduwa da cikas amma in ka samu nasara komai ya wuce. Ba za ka tuna wani abu ba, a rayuwa ta yau da kullum bana sanya abu a raina. Abu biyu ne kawai zan fadi a matsayin kalubalen da  na samu  a lokacin da aka kawo ni a matsayin shugabar wannan makaranta na samu matasa suna shigowa cikinta su yi kwallo. Akan lalata kofofin makaranta da tagogi ba wanda zai gyara, a kan haka makarantar take kazancewa ka samu kashi a ajin yara da kararen sigari da sauran abubuwan  kazanta, na nemi gudunmawar Hukumar Ilimin Bai-Daya a tsayar da wannan kwallon, na ci bakar wuya kafin samun nasarar hana buga kwallon. Sai kuma taron tattaunawa da kungiyoyi masu zaman kansu ke  yi a makarantar shi ma da goyon bayan Kwamishinan Ilimi aka magance matsalar.

Burina ya cika

Kashi 90 cikin 100 na burin da nake da shi a rayuwa ya cika, musamman a wannan makaranta da nake jagoranta, inda ta samu kyakkyawan yanayi cinkoson da ke cikin ajujuwanmu ya kau inda za ka samu yaro 35 zuwa 50 a cikin aji guda sabanin inda aka fito da za ka samu yaro fiye da 100 a cikin aji.

Abin da nake son a tuna da ni

Ni mace ce mai sakin fuska da mutunta jama’a a lokacin hulda, ba ni da wani abu da na sanya gaba kamar ci gaban karatun yara mata da maza. A kowane lokaci kwazona bai wuce yadda zan samar da ci gaba a tsakanin yaranmu mata. Na san malamanmu ba za su manta da ni ba yadda na aza hanya samun ci gaba a makarantarmu da fatan wanda zai gaje ni kada ya bari ci gaban ya tabarbare.

Wanda nake koyi da shi

Mahaifina nake koyi da shi, malamin makaranta ne da ya karantar a firamare da sakandare kuma ya yi aiki a Ma’aikatar Ilimi har ya zama mamba na dindindin, ni ce  na bi sawunsa sosai. Allah Ya jikansa da rahama

Shawarata ga mata

Mata su tashi tsaye su dage wajen neman ilimi, su yi wa ’ya’yansu tarbiyya tagari musamman ’ya mace. A yanzu mata matasa sun fara natsuwa suna son koyon sana’a don sun gaji da yin karamar murya. Sai dai akwai bukatar ci gaban ya wuce haka, akwai bukatar gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu su kara shigowa a tallafi karatun ’ya’ya mata. Da yawa akwai masu son karatun ba su da halin yi, idan za a rika samun tallafin, karatun mata zai bunkasa.