✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati da tsagerun Neja-Delta: Ba a kwace wa yaro garma?

Ga dukkan alamu za a fahimci irin abin da nake son fayyacewa duk da ban kasance mai bin diddigin tarihin wadancen tsageru da ke kokarin…

Ga dukkan alamu za a fahimci irin abin da nake son fayyacewa duk da ban kasance mai bin diddigin tarihin wadancen tsageru da ke kokarin gwada kwanji da hukuma kuma an ayyana neman hanyar sulhu sun ce a kai kasuwa. Duk da mai bukatar samun zaman lafiya a kasarmu Najeriya ne, saboda fitina an ce barci take, kuma wanda duk ya san illar ta ba zai nemi tashinta ba, amma abin takaici ne a ce ga wadansu mutane a wannan kasa suna cewa su ne wuka su ne nama ga duk wata kadara ko dukiya da ke karkashin kasa da aka gano a yankinsu. Sananne cewa wannan kasa tamu, a wannan yanki na Arewa ne aka yi amfani da nau’o’in abubuwan da suka gina tattalin arzikin kasar nan, wato gyada da auduga da fata da kuza da kuma komo a kasar Yarbawa, wadanda suka taimaka sosai wajen gina wannan kasa. Kuma an yi shugabanni masu kwazo da duk da sun kau, amma har yau idan aka ambace su sai ka ji tamkar suna raye, wato su
Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Sa Abubakar Tafawa balewa, ga Cif Obafemi Awolowo a Yamma da Zik a Gabas duk dai yau abin da suka yi sai dai a bi bayansu, amma butulci da hassada da rashin waiwayar alherin baya na ingiza wadansu da sunan a fasa kowa ya rasa ko a ba su arzikin yankinsu su kadai. Sun manta cewa tarihi na cike da cewa da wannan yanki na Arewa aka gina nasu yankin. D
Da fatar ni da duk mai son zaman lafiya za mu dukufa da addu’a da fatar samun nasara ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kan tsagerun yankin Neja-Delta masu kiran kansu NDA. Idan masu ganewa ne Allah Ya sa su gane su daina tayar da fitina, idan kuma tsautsayi ke kiransu, to an ce ba a kwace wa yaro garma, ga fili ga mai doki.
Allah Ka taimaki kasarmu da zaman lafiya tare da shugabanci wanda kowa zai amfana, kmin.
Mukhtar Ibrahim Saulawa, Katsina.
 07066434519, 08080140820.