Search
Subscribe
Gwamnati ta binciki kamfanonin da suke yin takin NPK –Sarkin Noman Bassa

Manoma a bakin aiki

Gwamnati ta binciki kamfanonin da suke yin takin NPK –Sarkin Noman Bassa

Sarkin Noman Bassa kuma Garkuwan Hausa/Fulani na yankin Pengana da ke Jihar Filato, Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi kira Gwamnatin Tarayya kan ta binciki kamfanonin da ta bai wa aikin yin takin NPK, a kasar nan game da irin takin NPK da suke yi.

Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi wannan kira ne a lokacina da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce kamfanonin da gwamnati ta bai wa dama su rika yin NPK, ba sa yin mai kyau. “Wani takin NPK da kamfanonin suke yi, idan ka duba za ka ga duk kasa ce a ciki.”

Ya ce sakamakon wannan zalunci da kamfanonin suke yi, manoma da dama suna yin asara saboda amfani da takin a gonakinsu.

Ya ce wannan matsala ta sa manoma suna guje wa takin NPK, da ake hadawa a Najeriya, suna sayen takin NPK da ake shigowa da shi daga waje da muguwar tsada.

“Don haka ya kamata gwamnati ta sanya ido kan wannan al’amari. Ta rika bin kamfanonin tana ganin irin takin NPK da suke yi, don magance wannan matsali,” inji shi.

Sarkin Noman ya ce matsalolin da manoman kasar nan suke fuskanta, su ne rashin taki da irin shuka da magungunan feshi da taraktocin noma da rashin tallafin gwamnati. Ya ce duk tallafin noman da gwamnati take bayarwa, ba ya isa ga manoma na ainihi, yana tsayawa ne ga manoma na takarda.

“Kamar ni a shekarar 2015 na noma masara buhu 920, a shekarar 2016 na noma masara buhu 930, a shekarar 2017 na noma masara buhu 997, bara na noma masara  buhu 966,  a bana ina sa ran zan noma masara  sama da  buhu 1000, amma ban taba samun tallafin komai daga gwamnati ba,” ini shi.                                                                                   Ya ce abin da gwamnati ya kamata ta yi, shi ne ta bi kauyuka ta binciko ainihin manoma, ta rika tallafa musu da taraktocin noma da taki da irin shuka da magungunan feshi da sauransu.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin