Categories: KungiyoyiSana'o'i

Gwamnati ta bukaci masu sana’ar faci su rike sana’arsu da gaskiya

Gwamnatin Tarayya ta bukaci ’ya’yan Kungiyar Masu Facin Taya a Najeriya su rike sana’arsu yadda ta dace saboda sana’a ce mai alfanu ganin tayoyin ababen hawa sun shafi rayuwar matuka da fasinjojin da ke hawa motoci da babura a kasar nan.

Babban Sakataren Ma’aikatar Kwadago ta Tarayya, Alhaji Amido Fantari ne ya yi wannan kira a jawabinsa wajen babban taron da kungiyar reshen Arewa maso Gabas ta shirya a ranar Asabar da ta gabata a garin Gombe.

ADVERTISEMENT

Alhaji Amido Fantari, ya ce Gwamnatin Tarayya ta damu matuka da yawan aukuwar munanan haduran abubuwan hawa da suke hallaka rayukan al’umma da dama a hanyoyin kasar nan sakamakon rashin inganci tayoyin mota da kuma na rashin kwarewar wadansu masu facin tayoyin.

Ya ce an fito da wasu sababbin hanyoyin koya sana’ar facin taya na zamani ganin yadda ake samun karuwar masu gudanar da sana’ar da ba su kware ba da suke yin sanadiyar jawo munanan hadurra a manyan hanyoyin kasar nan, inda ya bukaci su tabbatar sun dauki lokaci mai tsawo wajen koyon sana’ar kafin su fara aiki don a cewarsa gwamnati za ta rika sa musu ido a kan sana’ar.

ADVERTISEMENT

Daga nan ya tabbatar musu da cewa a shirye gwamnati take ta tallafa musu da kayayyakin sana’a na zamani da samar musu da rancen kudi don ba su damar bunkasa sana’arsu.

A jawabin Babban Ko’odinetan Kungiyar ta Kasa kuma Ko’odinetan Kungiyar a Shiyyar Arewa maso Gabas, Malam Abdurrahaman Yakubu, ya bukaci mambobin kungiyar a shiyyar su hada kai don samun ci gaba a sana’arsu.

Ya ce hadin kai a tsakanin mambobin musamman na halartar tarurrukan kungiyar ta kasa don sanin makaman aiki zai ba su damar bunkasa sana’arsu ta facin taya don samun ci gaba.

Malam Abdurrahaman ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai su rika tallafa musu da rancen kudi don ba su damar bunkasa sana’arsu ta facin taya wadda a cewarsa za ta taimaka wa al’umma baki daya.

Shugaban Kungiyar a Shiyyar Arewa maso Gabas Alhaji Sani Abdullahi, ya yaba wa shugabannin kungiyar ta kasa dangane da shirya taron a jihar, ya kuma bukaci ’ya’yan kungiyar a shiyyar da kasa baki daya su ci gaba da hada kai suna magana da murya guda don ta haka ne kawai za su samu ci gaba mai ma’ana a harkokinsu na yau da kullum.

A lokacin taron an rantsar da shugabannin kungiyar na shiyyar da suka hada da Alhaji Mamman Hussaini,  Mataimakin Shugaba da Yahaya Adamu, Sakatare da Kayode Ojo, Sakataren Kudi da Alhaji Abdulkadir Maigoro, Ma’aji da Baba Shehu Usman, Jami’in Hulda da Jama’a da Abubakar Abdullahi Ko’odineta da Malam Lawan Danladi, Mai bada shawara.

Uban Kungiyar na Kasa Alhaji Abubakar Abdulkadir, Yariman Gombe ya samu halartar taron.

. .

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago