✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta fallasa sunayen masu taurin bashi

A farkon wannan mako ne Hukumar Kula da Kadarori ta Kasa (AMCON), ta fara fallasa sunayen wadansu hamshakan ’yan Najeriya masu taurin bashin da suka…

A farkon wannan mako ne Hukumar Kula da Kadarori ta Kasa (AMCON), ta fara fallasa sunayen wadansu hamshakan ’yan Najeriya masu taurin bashin da suka ki zama tare da hukumar domin su warware ko su sauke nauyin da ke kansu.

Jadawalin sunayen mutanen tare da sunayen kamfanoninsu, har su 105, an buga su ne a ranar Litinin, kuma AMCON ta ce za ta shigo da hukumomin da suka dace a cikin wannan kiki-kakar, domin a tabbatar wadanda aka buga sunayen nasu sun biya basussukan da ke kansu.

Tun cikin watan Yulin da ya gabata ne, Babban Daraktan AMCON, Ahmed Kuru ya yi barazanar cewa zai buga sunayen kamfanoni da masu kamfanoni wadanda suka ki biyan dimbin bashin da ake binsu.

Na farko a jerin sunayen shi ne Ifeanyi Ubah, mai Capital Oil and Gas Industries Limited, wanda ake bin kamfaninsa bashin Naira biliyan 115. Sai kuma Jimoh Ibrahim mai NICON Inbestment Limited, Naira biliyan 59. Shi kuma Wale Babalakin mai kamfanin Bi-Courtney, ana bin kamfaninsa bashin Naira biliyan 40.

Cikin wadanda ake bi bashin har da Barth Enaji, tsohon Ministan Makamashi, wanda ake bin kamfaninsa Geometric Power Industries Naira biliyan 29.

Akwai ma inda sunan Babalakin ya sake fitowa, inda ake bin wani kamfaninsa bashin Naira biliyan 29. Sunan tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Chimaroke Nnamani ya fito, inda ake bin kamfaninsa mai suna Iorna Global Resources da wasu kamfanonin bashin Naira biliyan 42.

Haka kuma ana bin kamfanin Buruji Kashamu bashin Naira biliyan 13 da miliyan 15, sai kuma kamfanin Joshua Dariya, tsohon Gwamnan Jihar Filato da ke zaman kaso na shekara 14, shi ma ana bin kamfaninsa bashin Naira biliyan 6 da miliyan 800.

sai dai kuma Babalakin ya musanta cewa ana bin kamfaninsa na Bi-Courtney bashin kudi, cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai, ya ce AMCON ba ta bin Bi-Courtney bashin ko sisin kwabo.