Search
Subscribe
Gwamnati ta hukunta malaman jami’a

Gwamnati ta hukunta malaman jami’a

Assalam Edita. Gaskiya ina bakin cikin da irin hukuncin da ake yi wa malaman Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a kan lalata ko fyade ga ’mata dalibai, inda bayan makaranta ta kore su sai kotu ta tilasta a dawo da su bakin aiki. Ina kira ga hukumar makarantar ta rika daukaka kara kuma ya kamata Gwamnatin Taraya ta nada kwamiti da zai rika bincike a kan halin da mata ke samun kansu a manyan makarantun Najeriya. Domin da yawa suna faduwa jarrabawa  ce saboda ba su yarda malami ya yi lalata da su. Allah Ya shiryi wadanan miyagun malamai idan masu shiryuwa ne. Sannan akwai kungiyoyin malamai da dalibai, ta yaya suke wannan lalata da mata a jami’a ko ta hanyar lalama, ko ta nuna kudi, ko hanyar fyade, muna kira ga shugabanin jami’o’i, su ji tsoron Allah su da ’yan kan zaginsu dalibai su guji wannan mummunar dabi’a.

Daga Abubakar Hassan Muhammad Dori. 08068968317.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin