✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta kwato fiye da Naira biliyan bakwai daga wurin Diezani

Tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Misis Diezani Allison-Madueke wacce ta yi asarar biliyoyin kudi da gidajen alfarma sakamakon ummarnin da kotu ta bayar kwanannan na…

Tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Misis Diezani Allison-Madueke wacce ta yi asarar biliyoyin kudi da gidajen alfarma sakamakon ummarnin da kotu ta bayar kwanannan na mika kadarorin ga Gwamnatin Tarayya  a jiya ma ta sake sallama Naira biliyan bakwai da digo shiga ga gwamnati.

Ummarnin kotun na mika kudin ga gwamnati ya fara farkon shekarar da muke ciki lokacin da Hukumar EFCC ta nemi kotun ta kwato kadarorin da kudin a madadin gwamnati.

A jiya Mai Shari’a Abdulazeez Anka na kotun Gwamnatin Tarayya da ke Legas ya bayar da ummarni na karshe na mika Naira biliyan bakwai da digo shida kacokan ga Hukumar EFCC yayin  da aka rasa wanda ya yi ikirarin kudin nasa ne bayan wasu lokuta.

Hukumar EFCC ta fada wa kotun cewa binciken da ta gudanar ya gano cewa makuden kudin wadanda aka boye su a asusun bakuna daban-daban an same su ne ta hanyar almundahana.

Hukumar EFCC ta ce Diezani ta sace kudin ne ta hannun Tsohon Shugaban Sashen Kasuwancin Danyen Mai na Kamfanin NNPC, Gbenga Olu Komolafe da Tsohon Shugaban Kamfanin Lura da Albarkatun Mai na PPMC, Prince Haruna Momoh da kuma Shugaban Kamfanin Sayar da Taceccen Mai na NPMC .