Categories: KungiyoyiSana'o'i

Gwamnati ta sake tunani kan daina sayar da Dala ga masu shigo da kayan abinci

Shugaban Kungiyar Masu Shayi ta Najeriya, Alhaji Shu’aibu Abubakar, ya yi kira ga gwamnati ta sake tunani, kan sanarwar da ta bayar na daina sayar  da Dala ga masu shigo da kayan abinci daga waje da Babban Bankin Najeriya (CBN), yake yi.

Alhaji Shu’aibu Abubakar ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos, inda ya ce “Muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta sauya tunani kan umarnin da ta bayar na kada Bankin CBN  ya sayar da Dala ga wadanda suke shigo da kayan abinci daga waje.”

ADVERTISEMENT

Ya ce idan wannan umarni ya fara aiki, farashin  kayayyakin masarufi zai yi tashin gwauron zabo. Kuma idan farashin kayayyakin masarufi ya kara tashi, talakawa za su dada shiga mawuyacin hali a kasar nan.  Ya ce “Don haka muna  kira ga Shugaban Kasa da  ’yan Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai  su zauna su sake duba wannan al’amari, domin guje wa sake  dada jefa talakawan Najeriya A cikin mawuyacin hali.”

ADVERTISEMENT
. .

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago