✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta yi abu mai dorewa kan zaman lafiya a tsakanin makiyaya da manoma – Sale Bayari

Alhaji Sale Bayari  shi ne Shugaban Kungiyar Ci gaban Fulani ta Najeriya ta Gan Allah. A tattaunawarsa da wakilinmu ya nuna rashin gamsuwarsa kan abubuwan…

Alhaji Sale Bayari  shi ne Shugaban Kungiyar Ci gaban Fulani ta Najeriya ta Gan Allah. A tattaunawarsa da wakilinmu ya nuna rashin gamsuwarsa kan abubuwan da Kungiyar Fulani makiyaya ta  Miyetti  Allah ta Kasa, ta tattauna da jami’an Gwamnatin Tarayya a wajen taron da suka gudanar a Birnin Kebbi, kwanakin baya, kan matsalolin garkuwa da mutane da ake fama da su a Najeriya da rikice rikicen Fulani makiyaya da manoma. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

A matsayinka na daya daga cikin jagororin al’ummar Fulani a Najeriya, me za ka ce game da taron da kungiyar Fulani Makiyaya ta  Miyetti Allah ta yi da manyan jami’an Gwamnatin Tarayya a Birnin Kebbi,  kan  matsalolin garkuwa da mutane da hare-haren da ake kaiwa a kasar nan?

To kamar yadda muka karanta labarin wannan taro a jaridu da kuma al’ummarmu da suke wajen taron da muka tura, don su jiwo mana abubuwan da za su faru a wajen taron, a gaskiy mun dauka abubuwan da za a yi a wajen  taro, abubuwa ne na alheri. Amma daga baya da muka ji abubuwan da aka tattauna a wajen  taron, a ra’ayina na Shugaban Kungiyar Ci Gaban Al’ummar  Fulani ta Najeriya, ta Gan Allah,  ya zamo mini abin bakin ciki. Domin mun ji cewa ana zargin shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, sun je suna ciniki da Gwamnatin Tarayya, wai a ba su kudi su za su iya dakile ta’addancin da ake yi a cikin kasar nan, daga cikin al’ummar Fulani. Wannan abu ya ba mu mamaki kwarai da gaske.

Kuma suka ce suna magana da yawun al’ummar Fulani ne baki daya, suka nuna cewa duk fashin da ake yi da sace-sacen mutane da ake yi da kashe-kashen da ake yi a tsakanin Fulani makiyaya da manoma, Fulani ne suke yi. Wannan babban  bata sunan al’ummar Fulani makiyaya ne.  Da mun dauka za a je wannan taro ne domin a tattauna,  kan yadda za a samu zaman lafiya. Kuma a nema wa Bafulatani wajen da zai yi kiwo da burtali da zai tashi, idan ciyawa ta bushe ya fita ya yi wani wuri, kuma a samar masa mashaya. Abubuwan da  muka yi tsammani za a tattauna a wajen  taron ke nan. Saboda wadannan abubuwa ne za a yi amfani da su  yau da gobe, ta yadda ’ya’ya da jikokinmu za su amfana.

Amma ba wai ka dauki kudi ka bai wa mutum dan ta’adda mai kashe mutane da sace mutane tare da yin fashi, ka je ka ce kana ba shi kudi don ya daina wadannan abubuwa ba, idan ka ba shi kudi suka kare me zai yi? Abin da muka sani shi ne, babu kudin da za a bai wa wadannan mutane da ba za su kare ba. Saboda ba sana’a aka koya musu ba.

Wato a ganinka wannan abu da aka yi a wajen taron, an bata wa Fulani suna ne?

An bata mana suna sosai wanda za mu dauki shekaru  kafin mu gyara. Watakila sai mun  dauki shekara kamar 10 kafin mu gyara. Ko kuma idan muka samu shugabanni masu kishi na kwarai wadanda suka  san abin da suke yi.

To wadanne hanyoyi kake ganin gwamnati za ta  bi ta magance matsalar  rikice-rikice da garkuwa da mutane da ake zargin wadansu Fulani na yi?

To ni dai  gwamnatin nan tun farkon zuwanta a shekarar 2015, kafin a rantsar da Shugaban Kasa, akwai rahoton da na ba ta mai dauke da shafi 17, kan hanyoyin da za a bi a zauna lafiya a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan.  A lokacin na je na bai wa Shugaban Ma’aikata na Shugaba Buhari na lokacin, wato Shugaban Hukumar Kwastan na yanzu Kanar Hamidu Ali (mai ritaya). Bayan shekara daya na sake daukar wannan rahoto na kai musu, amma har yanzu shiru. Idan da sun aiwatar da kashi 15 cikin 100 na wannan rahoto, ina tabbatar maka da abubuwan nan ba su baci haka ba. Na je Jihar Zamfara a shekarar 2013 lokacin da Janar Aliyu Gusau ya tura ni Jihar ya hada ni da Gwamnan Jihar, don gano abubuwan da suke kawo rikice-rikice a tsakanin Fulani makiyaya da manoma. Da gwamnatin Zamfara  ta yi amfani da rahoton da na bayar a lokacin,   da abin da za ta kashe ba zai wuce Naira miliyan 47 ba.

Saboda haka gwamnatin nan akwai shawarwari da muka ba ta, kan kananan hukumomi 105 na jihohi 21 na  kasar nan, inda ake da matsala tsakanin Fulani makiyaya da manoma.  Na fadi ga abubuwan da suke faruwa da idan ba a tare ba, ga abubuwan da za su biyo baya. Ko sau daya ba a kira ni ba, ko ta waya a ce an ga rahotona an gode.

Don  haka abin da ya kamata a yi a kasar nan shi ne a yi zama na Fulani makiyaya da manoma a karkashin Gwamnatin Tarayya. Domin a tattauna  yadda za a yi mu hadu a gaya wa juna gaskiya, kan yadda za a zauna lafiya, kamar yadda ake zaune lafiya a baya.

Mu abin da muke so gwamnati ta tabbatar ta yi abin da zai taimaka wa al’ummar Fulani domin mu samu mu zauna lafiya a tsakanin Fulani makiyaya da  manoma a kasar nan, in da duk ake noma a kashi 100  a ce za a bai wa Fulani makiyaya kashi 30,  mu kuma mu tsaya daidai kashi 30 din, kashi 70 na manoma. A wani wuri kuma a kashi 100 a bai wa Fulani kashi 70, saboda ba a noman kirki a wajen, idan aka yi haka aka kebe mana irin wadannan wurare, za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan. Ba wai wata jiha saboda kabilanci ta ce ta hana kiwo ba, wannan ba zai kawo mana zaman lafiya ba.

Idan ka dauki dukkan kudin Najeriya ka bai wa ’yan ta’adda Fulani wadanda shanunsu suka kare a fadace-fadace a tsakanin Fulani makiyaya da manoma, babu abin da zai yi dangane da zaman lafiyar Fulani makiyaya da manoma. Don haka  idan ba wannan gyara aka yi ba, babu yadda za a cimma nasara.

Saboda haka gwamnati ta yi abu mai dorewa kan zaman lafiya a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan.