Search
Subscribe
Gwamnati ta yi watsi da batun zogale – Manoma

Gwamnati ta yi watsi da batun zogale – Manoma

Shugaban Kungiyar Manoma da Masana’antun Zogale ta Najeriya, Mista Michael Akoloaga Ashimashiga, ya nuna bacin ransa kan halin ko oho da gwamnati ke nunawa wajen samar da zogale duk da kiraye-kirayen da masana ke yi kan a dubi harkar noman zogale saboda abu ne da ke samar da kudi a yanzu.

Shugaban ya ce, duk da rahotanni da aka samu na bunkasar noman zogale an bar manoman zogale na Najeriya a baya. “Mun fahimci gwamnati ba ta da ra’ayi kan rahotanni da aka ba ta kan alfanun noma zogale, ba ta nuna wani ra’ayi don karfafa manoman zogalen. Muna da mambobi kusan dubu biyar; mun fito da shirye-shirye masu yawa kan yadda za mu shigo da matasanmu cikin harkar noman zogale a Najeriya,” inji shi.

Mista Michael Ashimashiga ya ce ya zauna da masu sayen zogale da dama a kasashen waje don magance wannan koma-baya tun da ya fahimci gwamnatin Najeriya ba ta da wani tsarin zuba jari don taimakon manoman zogale duk da yana da dimbin masaya, lamarin da ya ce ya sanya jikinsa ya yi sanyi.

Shugaban ya ce dukkan hukumomin gwamnati masu alaka da su sun kasa tabuka abin a-zo-a-gani ga manoman zogale. Ya ce “Idan manomi ya noma fili daya duk yadda zogale ya lalace, mun sani sai daya bisa ukun itacen zogale ya ba ka sama da kilo daya na haki. Kuma itacen zogale 25 za su ba ka kilo daya, lissafa itatuwa 25 zai ba ka tsakanin dubu 25 ko 28 ga kowane itace 1,100 da ka sanya a filinka na noman zogale.”

Mista Ashimashiga ya ce tsara gonar zogale guda zai iya lashe sama da Naira dubu 300; amma idan aka duba kudin sun yi yawa ga matasan da ba su da aikin yi. ya ce sun yi yarjejeniya da masu zuba jari, don samar da wuraren noma a kasar nan – inda za a bai wa matasa irin noma kyauta don su fara nomansa.

Ya ce kungiyar ta ce za ta kaddamar da rabon irin zogale biliyan tara ga kananan hukumomi 774 na Najeriya. Ya ce ana ganin hakan zai samar da sauki ga masu noman zogale musamman matasan da ake son shigowa da su cikin harkar.                                                                                                                                             Ana sa ran kasuwar zogale a fadin duniya ta samar da yawan zogale da za ta kai Dalar Amurka biliyan bakwai (kimanin Naira tiriliyan 2.52) zuwa karshen bana-wanda hakan ke nuna bukatar zogalen ya karu ke nan, daga biliyan hudu na Dalar Amurka a shekarar 2015.

Kasuwar Duniya ta bayyana cewa a kasar Indiya, a shekarar 2018 an samu Dala miliyan 70 kan fitar da zogale zuwa kasashen waje. Karin kashi 10 daga abin da aka fitar a shekarar 2017 wanda aka samu Dala miliyan 60.

Samar da zogale da ya kunshi gari da mai da ’ya’ya da ganyenta, bukatarsu na karuwa sosai saboda amfanin marasa lafiya.

A rahoton Kasuwar Binciken Harka Noma ta Duniya  (Technabio), ta bayyana kasuwar zogale ta duniya da cewa tana bunkasa da kusan kashi 10 a bana, kuma babban abin da zai  kara bunkasar kasuwar zogale shi ne a samu karin wayar da kai na sanin amfanin zogale ga lafiyar mutum.

Duk da tagomashin da ke akwai a kasuwar zogale musamman a kasashen Turai da Amurka, sai ga shi gwamnatin Najeriya ta hanyar Ma’aikatar Gona da Ci gaban Karkara ta gaza  samar da tsarin da zai ba manoman zogale na Najeriya amfani da damarmakin da ke manyan kasuwannin Turai da Amurka.

Najeriya na cikin kasashe da ke da nau’in zogale daban-daban a duniya, kuma har yanzu manoman na kwance a kasa domin gwamnati ta fita batunsu, ba tare da wani ingantaccen tsari mai dorewa da zai samar da amfani gare su ba.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin