✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta kawo karshen ‘yan bindigar Zamfara- Matawalle

Sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Mutawalle, ya ce zai yi duk maiyuwa wajen magance matsalar tsaro. Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan rantsar da…

Sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Mutawalle, ya ce zai yi duk maiyuwa wajen magance matsalar tsaro.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan rantsar da shi a matsayin sabon Gwamnan jihar a Gusau babban birnin jihar, kuma ya bukaci ‘yan bindigar jihar da su mika wuya sannan su canza yanayin gudanar da rayuwarsu saboda karshen ya zo.

Gwamna Bello, yua kara da cewa, gwamnatin za ta yi kokari wajen ginawa ‘yan gudun hijira gidaje tare da mayar da su garuruwan su.