Search
Subscribe
Gwamnatin Angola ta karyata rahotannin haramta Musulunci

Gwamnatin Angola ta karyata rahotannin haramta Musulunci

kasar Angola ta karyata rahotannin da ke nuni da cewa ta haramta addinin Musulunci a kasarta, sannan ta fara rusa masalaltai, a cewar Manuel Fernando, Darakta a ma’aikatar Al’adu da Harkokin Addini ta kasa.
Wani mazaunin gundumar Uige a garin Carmona, ya bayyana wa tashar yada labarai ta Aljazeera, cewa masallatan da aka rufe, wasu baki ne kwararrun ma’aikata ’yan kasashen waje suka yi saurin ginasu, don suna bukatar wurin yin sallar Juma’a, kuma mafi yawancinsu, sun fito ne daga kasashen Afirka ta Yamma da Arewacin Afirka.
“Babu yaki a kasar Angola da Musulunci ko kuma wani addini,” a cewar Fernando, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP. Sai dai babu wani matwsayi da hukuma ta dauka game da rushe wuraren ibada, a ko’ina suke,” inji shi.
Sai dai wata mujalla a Angola da ake yi wa lakabi da Edame Angola, ta ruwaito cewa an rufe wani masalalci a garin Huambo, “a karkashin umarnin hukumomin ’yan sandan gundumar Huambo,” kamar yadda daya daga cikin shugabannin masallacin ya bayyana, ita kuwa jaridar Edam eta ruwaito, inda ta bayyana cewa shi ne masallaci na 60 da aka rufe.
Wani babban jigo a cikin Musulmin Angola, Dabid Ja ya bayyana cewa gwamnati na amfani da siyasa wajen tursasa musu, tare da “nuna kiyayya ga addininsu,” kamar yadda AFP ta ruwaito, inda ta bayyana cewa ya yi watsi da karyatawar da Fernando ya yi, cewa Gwamnatin Angola tana musguna wa Musulmi.
Tun a shekarar 2008. Aka kididdige yawan Musulmin kasar, inda aka gano cewa a cikin mum miliyan 18 na al’ummar kasar, mutum dubu 90 ne Musulmi, kamar yadda sashen tattara bayani na Gwamnatin Amurka ya tabbatar.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin