✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Bashar assada ta sauya wa makamanta wuri

Sojojin Bashar al-Assad ta kwashe jami’ai da makamanta daga hedkwatar soja da harkokin tsaro da ke tsakiyar birnin Damascus, a shirin da take na tunkarar…

Gidajen Siriyawa da yaki ya rusaSojojin Bashar al-Assad ta kwashe jami’ai da makamanta daga hedkwatar soja da harkokin tsaro da ke tsakiyar birnin Damascus, a shirin da take na tunkarar harin da kasashen Turai da Amurka ke shirin kawo musu, a cewar mazaunan birnin da ’yan tawaye. Domin an tabbatar akwai yiwuwar kawo wa kasar hari a karkashin jagorancin Amurka, ta hanyar hadin gwiwar Turai da Amurka da kawayensu na Gabas ta Tsakiya, wadanda suka dora alhakin amfani da iskar gas mai guba da aka harba wa faraern hula a Siriya, kan sojojin kasar.
Gine-ginen da aka kwashe mutane da kayan cikin, sun hada da Babbar Cibiyar rundunar soja da ke dandalin Ummayyad da rundunar sojan sama da cibiyar tsaro da ke Yammacin gundumar Kfar Souseh, kamar yadda ’yan tawayen Siriya suka bayyana.

…Amurka na ruruta wutar yakin kai wa Siriya farmaki

kasar Amurka da kawayenta sun shirya kai wa Siriya hari, kasashen da ke gaba-gaba sun hada da Faransa da Birtaniya, sai kuma sauran Larabawan da ba sa ga maciji da Al-Assad, wadanda suka hada da Saudiyya. Amurka sai rura wutar yaki take yi, don ksai hari Siriya, sai dai tana takatsantsan kada a sake kwata Afghanistan da Iraki.
Sakataren tsaron Amurka Chuck Hegel ya ce sojojin Amurka na yankin Gabas ta Tsakiya suna cikin shiri, da zarar Shuaba Barack Obama ya ba su umarni. Obama dai ba ya son yin gaban kansa, inda yake shirin kulla kawance da kasashen Birtaniya da Kanada. Su kuwa jami’an asirin Amurka suna tattara bayanan da za su kafa hujja da su, don kai wa Gwamnatin Siriya, inda za su tuhumeta da yin amfani da makamai masu guba. Domin mai Magana da yawun fadar White House, Jay Carney ya ce “wauta ce” ma a yi tunanin cewa wani ne ba sojojin Assad suka yi amfani da makamai masu guba ba.
Sai dai Firayiministan Birtaniya, Dabid Cameron, na yin takatsantsan kada ya samu kansa a ta saka mai wuya, tamkar yadda Gwamnatin Obama ta samu kanta a Afghanistan da Iraki.
Shugaban ’yan tawayen Siriya, Ahmad Jarba, ya gana da jakadun kasashe 11 a Otal din Istanbul, wadanda suka hada da Jakadan Amurka a Siriya, Robert Ford. Shugaban ’yan tawayen, ya wassafa musu wuraren da ya kamata akai hari da makami mai linzami.
Tuni Gwamnatin Siriya ta karyata zargin da ake yi mata na amfani da makamai masu guba. Kuma kasashen rasha da Iran na goyon bayanta. Su ma sun ja daga, inda suka nuna rashin amincewarsa da harin da Amurka da kawayenta na Turai ke shirin yi.
Gwamantocin Masko da Beijin da ke da kujera a Majalisar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya sun ki amincewa da wannan shirin. Don haka wannan hari bai samu amincewa majalisar tsaron ba.
Kasuwannin hada-hadar kudi sun fadi, a sanadiyyar dar-dar din aukuwar yakin duniya. Sai dai farashin mai ya karu fiye da yadda yake a watanni shida da suka gabata. Hauhawar farashin man fetur ta cutar da kasar Turkiyya da sauran kasashe masu bunkasar tattalin arziki.