Da Dumi Dumi

Gwamnatin Bauchi ta dauki aniyar mayar da yara sama da miliyan 1 makaranta – Surumbai

Dokta Abubakar Surumbai Sheikh Dahiru Bauchi
Dokta Abubakar Surumbai Sheikh Dahiru Bauchi

Wani bincike da aka yi ya nuna cewa Jihar Bauchi na fama da yara sama da Miliyan daya da dubu 300 da ba sa zuwa makaranta. Dokta Abubakar Surumbai Sheikh Dahiru Bauchi shi ne Shugaban Hukumar Ilimin bai daya (SUBEB) na Jihar Bauchi. A cikin zantawar da ya yi da manema labarai, ya fayyace irin matakin da suka dauka da kuma yadda suka tunkari al’amarin.

Kimanin wata uku ke nan da zama Shugaban Hukumar SUBEB, ko yaya ka sami harkar ilimi a jihar?

Alhamdulillahi, tun lokacin da wannan gwamnati ta shigo na mai girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed mun yi tsare-tsare iri-iri bisa irin matsalar da shi gwamnan ya gada kan ilimi. Da farko gwamnatinsa da ta zo ta samu makarantun Jihar Bauchi da yawansu iska ta yaye rufinsu kusan shekara biyu ba a gyara ba, kuma ta samu azuzuwa babu kujerun zama, makarantun ba kayayyakin koyon karatu ba kuma na koyarwa. Wadannan matsaloli duka a matakin firamare da karamar sakandare  ke nan, don su ne ke karkashin kulawar hukumarmu, sauran makaranru na babban sakandare da na gaba da sakandare suna karkashin Ma’aikatar Ilimi. Da Allah Ya kawo wannan gwamnati sai abin ya damu mai girma gwamna, sai ya tunkari matsalar, irin tunkarar da ba a taba yin irin ta ba, inda ya tafi Abuja har hukumar UBEC ya kasa, ya zauna da su ya nemi daukinsu. Ya kuma dawo gida duk da matsalolin kudi da jiha ke fuskanta ya samo kudi ya biya kason Jihar Bauchi, su ma Hukumar UBEC ta sa na ta. Ya bada ayyuka dabam-dabam na gyaran makarantun firamare da tona musu rijiyar burtsatse da gina sabbin ajujuwa. Kusan ayyuka dabam-dabam guda 950 ya bayar kan kudi sama da Naira Biliyan biyar da Miliyan dari biyar. Yanzu haka ana kan gudanar da wadannan ayyuka wasu an kammala wasu kuma ana cigaba da ayyukan, yanzu haka in kai dan Jihar Bauchi ne ko bako in ya shigo jihar zai shaida kuma zai ga canji a makarantun firamare da na karamar sakandare da ke jihar saboda sabbbin ayyuka da suka bayyana. Kuma gwamna ya yi gagarumin shirin cikin shekara da 2020 don gina manya-manyan azuzuwa da karasa gyare-gyaren makarantun domin mayar da dalibai makaranta da samar da wuraren koyon ilimi masu nagarta.

A kan samu matsalar yara sun gama firamare da sakandare ba su iya karatu ba, ko kun lura da wannan matsala kuma yaya kuke yi da ita?

Gaskiya mun lura da ita, tana daga cikin matsalolin da muka gada. Lokacin da na kama aiki na kai ziyara makarantun firamare a Jihar Bauchi da kaina na yi ta daga yara cikin azuzuwa wasu suna da kokari wasu kuwa an tafi an bar su a baya. Da muka ga wannan matsala muka dauki damara don horar da malamai yadda ya kamata kuma mun baiwa malaman shawarwarin yadda za su inganta ayyukansu kuma nan gaba duk makarantan da muka je idan muka samu irin wannan za mu kama malamin da kuma shugaban makarantan da laifin gazawa.

ADVERTISEMENT

Matsalar kujeru da tebura fa, an ce yaran a kasa suke karatu wasu kuma a gindin bishiya?

Gaskiya ne akwai wannan matsala, shi ma haka muka gaje shi, sai dai muna kokarin sauya yanayin in Allah Ya so cikn wannan shekarar ta 2020 za mu roki gwamna ya amsar mana da kudi da za a samar da kujeru da tebura a makarantun, kuma a duk inda na je nasamu wannan matsala nakan roki shugaban makarantan da iyaye da masu ruwa da tsaki cewa mu yi kokari a hada hannu a kula da dukkan kayayyakin da gwamnati ta gina a makarantu, koda kwano ne ya fara dagawa ya kamata al’umma su dauki makarantun na su ne, kada su bari a rika lalata su ko a sace su.

Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da ke fama da yara da a wani kiyasi aka ce sun kai sama da miliyan daya da dubu 300 da ba sa zuwa makaranta, yaya kuke tunkarar wannan lamari?

Alhamdulillahi tun zuwan wannan gwamnati wannan abu ya dami mai girma gwamna, kuma yana ta kokari sai Allah Ya dubi niyyarsa ya kawo mana dauki cikin wani shiri na samar wa al’umma ilimi mai nagarta BESDA, shiri ne da zai kwashe wadannan yara ya mayar da su makaranta, shirin hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Tarayya da na jihohi. Lokacin da na zo akwai koma baya cikin wannan shiri sai muka ja damara tunda shi gwamna ya kaddamar da shirin kwanan baya a garin Alkaleri, na jagoranci gangamin wayar da kai a koma makaranta zuwa masarautun Jihar Bauchi guda shida, kuma na ziyarci tsangayu muna kuma shirin zuwa wuraren talla kamar kasuwanni da tashoshin mota. Alhamdulillahi wannan shiri ya samu karbuwa wajen masu makarantun tsangaya da kuma su sarakunan, a yanzu haka cikin watan Disamba mun samu dalibai sama da dubu 120 da za a mayar da su makaranta, duk da cewa abin da ake sa ran za mu mayar da sune yara dubu 68, daga cikin dubu 33 maza dubu 25 kuma mata wadanda ke tsakanin shekara biyar zuwa shekara 15 wadanda lokacin da muke tantance tsangayu muka same su. Kuma karkashin wannan shiri an fara gina azuzuwa na wucin gadi a wuraren da babu azuzuwan kuma Alhamdulillahi lokacin da gwamna ya sanya hannu kan kasafin kudi kowa ya ji irin himmarsa, inda ya ce za a gina manyan azuzuwa don mayar da wadannan yara makaranta.

An ce a baya masu ruwa da tsaki cikin makarantun tsangaya ba su ba da hadin kai?

Haka ne amma a wannan karo ka ga mun samu malaminmu Shehu Dahiru Bauchi tun ranar da gwamna ya fara kaddamar da wannan shiri ya wayar da kan al’umma wanda maganganun da ya yi, sun yi tasiri domin ya ce kowane mutum ya kamata ya zama mai hannu biyu, hannun dama ya dauki ilimin addini hannun hagu ya yi ilimin boko amma in ya zama mai hannu daya, da shi zai yi tsarki da shi zai ci abinci ka ga baiyi ba. Don haka dole ne a yi ilimin addini kuma dole ne a yi ilimin neman zaman duniya kar mutum ya samu koma baya ana ce masa direban hajiya ko mutum mai wani sana’a makaskanci saboda rashin ilimi.

Mun shaida wa masu tsangayu cewa wannan shiri ba zai shafi lokacin yin karatunsu ba amma za su bada wasu ’yan awoyi cikin lokutan da ba sa yin karatu domin a yi musu darasin boko kamar na lissafi da turanci, kuma malamin ma zai samu fa’ida, inda za a ciyar da daliban kuma za a duba matsalolin makarantun tsngayar. Wanda ba ya da bayangida a yi masa, wanda ba ya da rumfa a masa, har rijiyar burtsastse za a musu kuma za a ciyar da daliban abinci kyauta kuma malamin za a bashi alawus. Yanzu an yi nisa saura a fara karatu cikin wannan watan Janairu da muke ciki in Allah Ya so, tuni an horar da malamai sama da 3382 da masu horarwa mutum 70 da kuma masu sa ido da kula da ayyukan su 246.

A karshe wace shawara za ka ba iyaye?

Shawarwarin su ne, a’lumma su ba mu hadin kai su fahimci ayyukan da ake yi nasu ne. Su kuma ’yan kwangila, ya kamata su ji tsoron Allah, an ba su wannan aiki ne don su ma su samu amfani, bai kamata su yi mummunar aiki ba.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya