✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake rufe wuraren ibada da kasuwanni a Binuwai

A wani mataki mai kama da kwan-gaba-kwan-baya, gwamnatin jihar Binuwai ta sanar da sake garkame wuraren ibada da kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a da…

A wani mataki mai kama da kwan-gaba-kwan-baya, gwamnatin jihar Binuwai ta sanar da sake garkame wuraren ibada da kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a da aka bude tun da farko don takaita yaduwar cutar Korona.

Matakin dai na zuwa ne bayan da gwamnatin ta bude wuraren da tun da farko ta rufe da zimmar takaita yaduwar cutar.

Gwamanan jihar, Samuel Ortom shi ne ya sanar da hakan yayin jawabi ga ‘yan jarida a fadar gwamnatin jihar da ke Makurdi.

Ya ce gwamnatin ta yanke hukuncin ne bayan shawarwarin da ta samu daga gwamnatin tarayya da kungiyoyin addinai a jihar kan sake bude wuraren.

Ya kara da cewa jihar ta sa za ta yi aiki kafada da kafada da dukkan masu fada a ji, ciki har da Hukumar Da Ke Kula Da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) don kawo karshen annobar.

Ortom ya ce, “A madadin Majalisar Zartarwa ta jihar Binuwai, ina sanar da dawo da dokar hana taruwa a masallatai da coci-coci da kasuwanni.

“Saboda haka daga yanzu wadannan wuraren ibada da kuma kasuwanni za su ci gaba da zama a rufe.

“Wannan dokar ta shafi taron jana’iza, bukukuwan daurin aure da sauran tarukan jama’a da muka ce kada a zarce mutum 30 tun da farko.

“Muna bukatar al’umma ta fahimci cewa wannan annoba gaskiya ce, ba ta da magani kuma tana kisa, amma akwai matakan kariya da masana harkar lafiya suka ba da shawara”, in ji gwamna Ortom.

A wani labarin kuma gwamna Ortom ya tabbatar da cewa matar da aka tabbatar ita ce ta uku mai dauke da cutar a jihar, Misis Rebecca Apedzam ta warke kuma an sallame ta ranar Litinin.

Misis Apedzam wadda tsohuwar kwamishina ce a jihar kuma tsohuwar ‘yar majalisar tarayya a jamhuriya ta uku an tabbatar ta na dauke da cutar ne bayan da aka gwada ta ranar 11 ga watan Mayun da mu ke ciki.